Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakolo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne game da ‘ya’yan da ba sa jin maganar Iyayensu, za ku ga suna ba wa Iyaye wahala da tashin hankali
Usman Sani
Akwai dalilai daban-daban da ke sa wasu ‘ya’ya ba sa jin maganar iyayensu, kuma suna da alaka da halaye, yanayi na rayuwa, da kuma yadda iyaye suke gudanar da tarbiyyar yara.
Ga wasu daga cikin dalilan:
- Rashin kyakkyawar sadarwa: Idan babu kyakkyawar fahimta tsakanin iyaye da yara, yara za su iya jin kamar ba a sauraron ra’ayinsu ko matsalolinsu, wanda zai iya sa su bijirewa umarni.
- Yanayin Tarbiyyar Iyaye: Wasu iyaye suna yin amfani da hanyoyi masu tsanani wajen koyarwa ko hukunta yara, wanda ke haifar da tsoro maimakon kauna, har ya sa yaran su guji biyayya.
- Tasirin Abokai ko Muhalli: Yara suna iya samun tasiri daga abokai ko muhalli mai mugun tasiri, wanda ke sa su rinjayar da tunaninsu da halayensu fiye da iyayensu.
- Rashin Lokaci daga Iyaye: Idan iyaye ba sa daukar lokaci don kula da bukatun yara ko zama tare da su, yaran na iya jin kamar ba su da muhimmanci, wanda zai sa su dauki umarni da sakaci.
- Rashin Samun Tsayayyen Jagoranci: Idan iyaye suna da rauni wajen tsayar da dokoki ko ka’idoji a gida, yara za su iya samun ‘yancin yin duk abin da suke so ba tare da tunanin sakamako ba.
- Yara Na Gwajin Iyakokinsu: Wasu yara suna gwajin iyakokin iyayensu don ganin yadda za su amsa. Wannan na iya zama al’ada ta girma da koyon ‘yancin kansu.
- Zamanin Fasaha da Social Media: Wannan zamani ya kawo yawaitar amfani da fasaha da kafofin sada zumunta, wanda ya janyo hankalin yara daga jin maganar iyayensu.
- Rashin Kula da Kwarewar Yara: Idan iyaye ba sa la’akari da bukatun yara da halayensu na musamman, hakan na iya haifar da rashin fahimtar juna, wanda ke rage jin maganar iyayen.
Hanyoyin Magancewa
Samar da kyakkyawar sadarwa tsakanin iyaye da yara. Nuna kauna da fahimta a duk al’amuransu.
Fa’isa Musa
Na farko dai abin da ya sa nake ganin wasu yaran ba sa jin maganar Iyayensu shi ne, gaskiya na fi ba wa Iyayen laifi saboda wasu iyayen za ki ga ba sa tsawatar wa ‘ya’yansu tun fatko, sai su ga kamar soyayya ce, ba za su tsawatar musu in yaro ya yi abu sai a bar shi, sannan kuma ba sa bukatar kowa ya tsawatar musu.
Za ki ga uban ko uwar wani ya tsawatar musu sai ki ga ransu ya baci.
To kuma tarbiyya mutum daya ba ya tarbiyya sai ka hada da addu’ar, sai ka bari wani na kusa da kai ya taya ka sai kuma ka tsawatar gaskiya.
Sannan abu na biyu abin da ke kawo rashi jin yaro shi ne aibata yaro ko zagin sa in ya yi wani abu , don da yawa daga cikin iyaye wasu musamman wanda ba su da addini ko karancin sa to ba sa iya bakinsu akan yaro.
Idan yaro ya yi abin da ya bata musu rai ko wani abu ba za su iya nusar da shi su yi masa nasiha ba sai dai zagi, wani lokaci za ki ga ga uwa ta zagi yaro da sunan uba ko kuma uba ki ga ya zagi yaro da sunan uwa wata ma har ki ga bacin rai ta tsinewa da to ya za a yi da ya yi abin da kike so ko kuma ya ji magana saboda bacin rai ya sa kin buda baki kin mishi baki ko ka masa baki, shi bakin iyaye wani abu ne da yake tasiri akan yaro fiye da komai a rayuwar sa, duk abin da yaro ya yi shi ne ka hada shi da addu’a ka zaunar da shi ka yi masa nasiha in yana lokacin da ya kamata ka buga ne idan abin da ya yi ya sa mata ka buga ne sai ka buga ka nuna masa kuskurensa.
Akwai lokacin da yaro ya wuci buku to ko ka buge shi ma ba ji zai yi ba, wannan sai ka jawo shi a jiki da nasiha, saboda abokai ma suna yi wa yaro tasiri sosai a rayuwa.
Sannan ya kamata ka kula sosai da wa yake mu’amala ya danganta da wanda yake mu’amala da su in na kwarai ne to shima zai zama na kwarai in na banza ne zai zama na banza, don haka ya kamata iyaye su lura da wannan abu ukun, na farko su kiyaye san da ya yi yawa su bayyana soyayyar sa ta inda wani bai isa ya kwabe shi ba ko su ba za su kwabe shi ba to.
Na biyu kuma, su hada masa da addu’a sannan su kiyaye furucin da za su yi akan sa. Na uku kuma shi ne su kula da wa yake mu’amala wane ne abokinsa, aboki na kwarai zai zama na kwarai, aboki na banza zai zama na banza, don haka wannan yana da tasiri sosai akan yara ya kasance kuma koda yaushe kana jan su a jiki kana yi musu addu’a, sannan ka zama ka sakin jiki da su duk abin da ya faru za su iya fada maka saboda zan iya cewa kaso tamani cikin dari na tarbiyya yaro yana daga wanda yake mu’amala da shi ko aboki ko wani abu, sannan baki kuma a kiyaye shi sosai in ba haka ba gaskiya shi yake tambadar da yaro. Allah ya shirya mana.
Maryam Umar
Wasu yaran laifin iyayan ne tun suna yara idan sun yi abu ba a tsawatar musu idan sun yi abu sai a yi musu dariya da haka yaro yake wucewa idan iyayen suka yi musu magana ba za su ji ba.
Wai ana gani shi yaro ne bai isa duka ba, amma ai ana farawa da dan yi tsawa ne da kadan-kadan tun yana karami kana nuna masa abin da yake daidai da abin da ba daidai ba har ya kai lokacin duka da kuma lokacin da ya wuce duka.
A gaskiya wannan dariya da akewa yaro idan ya yi abu ba karamin tambada yaro take ba saboda shi zai yi zaton komai na dariya ne.
Hassan Tijjani
Jin maganar Iyaye na da matukar muhimmanci a addinance, da al’adance.
Wasu ba sa jin maganar iyayensu saboda tsantsar shegantaka, da iskanci.
Wasu ba sa jin maganar iyayensu ne saboda su ma iyayen ba su darajanta kansu yadda ya kamata ba, ta yiwu ba sa komai kan dai-dai. Amma ko ya ya ne, rashin jin maganar Iyaye babban kuskure ne.
Bara’atu Amar
Yaran da ba sa jin maganar iyayensu suna iya yin hakan saboda dalilai daban-daban da suka danganta da tarbiyya, yanayi, ko halayensu na dabi’a. Ga wasu daga cikin dalilan:
- Rashin Kula ko Lokaci daga Iyaye: Lokacin da iyaye ba sa bai wa yara lokaci ko kulawa ta musamman, yara suna iya jin cewa ra’ayoyinsu ba su da mahimmanci, wanda ke sa su yi watsi da maganganun iyayensu.
- Tarbiyya mai Tsauri ko Sauki Mai Yawa: Idan iyaye suna da tsaurin kai ko saukin kai sosai, yara suna iya yin bore ko watsi da maganganu. Iyaye masu tsauri suna sa yara su ji tsoro ko su guje musu, yayin da masu saukin kai ke ba yara damar yin abin da suke so.
- Matsalolin Muhalli: Yanayi kamar rikici a gida, talauci, ko rashin zaman lafiya na iya tasiri kan halayen yara, wanda ke sa su kasa sauraron iyayensu.
- Tasirin Abokai ko Al’umma: Wasu yara suna iya yin tasirin abokai ko al’umma fiye da iyayensu, musamman idan suna ganin cewa iyayensu ba sa fahimtarsu.
- Rashin Sadarwa Mai Kyau: Idan iyaye ba sa iya bayyana kansu da kyau ko ba sa sauraron yaransu, yaran na iya jin cewa ba a ba su muhimmanci, wanda zai iya haifar da rashin biyayya.
- Yanayin Shekaru: Yara a lokacin balaga suna yawan gwada sabbin abubuwa da neman ‘yanci. Wannan wani lokaci ne da suke iya ganin kansu kamar sun san komai, wanda ke sa su yi watsi da shawarar iyaye.
- Rashin Darasi ko Horarwa: Idan iyaye ba sa koya wa yara mahimmancin biyayya da mutunta manya tun suna kanana, hakan yana iya tasiri kan halayensu yayin da suka girma.
Yadda za a magance matsalar:
A-Kula da yara da ba su lokaci mai kyau. B- Habaka sadarwa mai kyau da yaran. C-Nuna musu kauna da girmamawa. D- Sa su fahimci sakamakon rashin biyayya. E- Kauce wa tsaurin kai sosai amma a samar da iyaka. F- Neman shawara daga malamai ko masu ilimi idan matsalar ta yi tsanani.
To ta wannan hanya, za a iya taimaka wa yara su zama masu biyayya da mutunta iyayensu.