Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da sanya harajin fito na ramuwar gayya kan dukkan kawayen cinikayyarta a ranar 2 ga wata, inda kasar Sin ta mayar da martani nan take, da zummar kiyaye halastaccen hakkinta. Daga baya a ranar 3 ga wata, Sin ta sanar da wasu jerin matakai, ciki har da kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, da shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka, gami da kara wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin sunayen kamfanonin da ta dauki matakin hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a kansu, matakan da suka janyo babbar raguwar darajar takardun hannayen jari a Amurka.
Sin da Amurka za su iya cin gajiya daga hadin-gwiwarsu, amma dukkansu za su gamu da hasara in sun yi fada da juna. Manazarta na ganin cewa, matakin Amurka na kakaba harajin fito na ramuwar gayya, zai iya haifar da illa ga tattalin arzikin kasar Sin a cikin wani gajeren lokaci. Amma ganin yadda kasar ta Sin ta shawo kan sabanin kasuwanci sau da dama, dorewar tattalin arzikin kasar Sin na kara inganta. Kazalika, kwararan shaidu sun riga sun nuna cewa, kara sanya harajin fito da Amurka ta yi, ba zai daidaita matsalar rashin daidaiton cinikayya ba, sai dai kara illata tattalin arzikin kanta.
A halin yanzu, sassan kasa da kasa na kara yin mu’amala tsakanin juna, har ma tattalin arzikin duniya na kara dunkulewa waje guda. Ra’ayin daukar matakai na kashin kai, da ra’ayin kariyar cinikayya, sam ba za su samu goyon-baya ba. Ya dace Amurka ta gyara kura-kuranta, ta dakatar da yin amfani da batun kakaba harajin fito wajen tilasta wa sauran kasashe. Sa’an nan, ya dace sassan kasa da kasa su hada gwiwa, don adawa da irin bangaranci da babakeren da Amurka ta nuna, da ci gaba da kiyaye tsarin cudanyar kasa da kasa a fannin kasuwanci. Babu tantama, ba wanda zai yi nasara daga yakin harajin fito da yakin cinikayya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp