Barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da ‘Ramadan Basket’, inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; ‘Wane tanadi aka yi wa azumin watan ramadan?, Ya makomar ramadan basket yake a wannan lokacin?, Mene ne amfani ko rashin amfanin yin ramadan basket?.
- Kasar Philippines Za Ta Dandana Kudarta Game Da Gudummawar Soja Da Amurka Ta Ba Ta
- Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aminu Ilyas Isah (Farfesa), Jihar Kano, UGG, Zango Ward:
Shiri bai wuce na tsoron Allah ba, domin shi ne Allah ya ce “Duk wanda ya ji tsoron Allah to Allah zai bashi mafita”. ‘Yan mata sun saka ran a basu Ramadan basket, samari kuma babu kudade a hannunsu, ma’aurata suna siyan abin da Allah ya hore musu ne. Ga me hali sai ya yi wa iyayensa idan yana da wadata ya yi wa budurwarsa, domin yanzu sai mutum ya daddage ya yi wa yarinya amma ta dawo tana cewa ta wanki gara. Amfanin ramadan basket yana karin dankon soyayya, rashin amfaninsa bai wuce idan ka saba yi wa yarinya shikenan randa baka yi ba abin ya zama rigima har soyayya ta samu rauni.
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna:
Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan Ramadan din ba, kuma mu sa kasar mu cikin addu’a Allah ya bamu dacewa.
Sunana Abubakar Ahmad, daga Jihar Nassarawa:
Ga me hali ya kan shiryawa gajiyayyu marasa hali, wanda kuma Allah bai hore masa ba ya shiga sahun wanda sai dai a dauka a basu su wadannan ba sa shirya komai face yawan salloli da addu’o’i da neman taimakon ubangiji Allah ya fitar da su daga kangin talauci da suka samu kansu a ciki. A halin da ake ciki ramadan basket yana natukar wahala, tsakanin ‘yan mata da samari za a yi ta samun matsala a wannan lokacin, amma idan har soyayya ce ta gaskiya ya kamata ita budurwar ta fuskanci halin da ake ciki tayi hakuri ga dukkanin abin da ya samu, wani koda yanada halin yi akwai dawainiya da yayi masa yawa na iyaye ko ‘yan’uwa, ko kanne ko wata bukata ta kansa wacce yake ganin tafi mahimmanci a kan ramadan basket din.
Sunana Hassana Aminu Zubairu daga Jihar Kano:
A gaskiya duk wani musulmi kwarai yana shiri kafin gabatowar watan ramadan ,ya shirya wa ransa zai jajirce wajen bautar ubangiji domin neman kusanci da ubangiji. Yawan ci ‘yan mata suna shirin yin ibada da rokar miji nagari, wasu kuma suna shirin da karbar ramadan basket daga wajen samarinsu,haka suma samari wasu suna shirin ibada da rokar mace tagari sannan kuma wasu suna shirin farantawa yanmata su da ramadan basket. Ramadan basket ta wani fannin yana da amfani, domin farantawa dan uwanka musulmi yana da babban lada to, amma kuma ta wani fannin ba shi da amfani saboda yana zama kamar gasa ko karya, wane yayi abu kaza ni kuma na kere shi nayi wanda ya fi shi to, a gaskiya indai dan gasa za ai ko dan karya to a gaskiya gwara a hakura ba a yi ba.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To da farko shirin da aka yi wa wannan wata mai alfarma shi ne Allah ya nuna mana shi muna cikin masu rai da lafiya, bangaren kuma tanaji mun yi iya bakin gwargwado duba da irin halin da ake ciki na matsin tattalin arzikin dama tsadar rayuwa. To magana gaskiya batun Ramadan basket wani abu ne da idan mutum yana da hali babu laifi sai ayi amma idan babu hali sai ayi domin ana cikin wani yanayi na matsin tattalin arzikin da tsadar rayuwa abubuwa da dama da aka saba yi yanayi ya jawo an hakura da su. To amfanin sa kyautatawa ce a tsakanin masoya don haka idan da hali babu laifi sai ayi idan kuma babu hali sai ayi hakuri yau da gobe sai Allah. Sawara dai a nan ita ce; wannan wata ne mai alfarma na ibada don haka ya kamata mu dage da ibada da ayyuka nagari domin mu dace da falalar sa da kuma addu’a tukuru domin Allah ya kawo mana karshen matsalolin da suka addabi kasar mu Najeriya baki daya.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori:
Mukan zabi abun da ya fi muhimmaci mu bar wanda ba shi da muhimmaci ko kuma mai muhimmacinma, mu rage masa karfi, domin sassauta rayuwar mu da ta iyalanmu musamman a wannan wata namu mai albarka. Domin yin rayuwa daidai ruwa daidai tsaki. ‘Yanmata da samari da ma’aurata sukan sa ran dan wani abu na kyautatawa daga wajen masoyansu ta hanyar ba da (Ramadan Basket). Su ma samarin sukan sa ran kayan bude baki daga wajen ‘yanmatan su. To ina kira ga samari da ‘yanmata da ma’aurata da ku tsaya a inda Allah ya aje ku kada ku yi abun da za ku takura kanku, kowa ya san halin da ake ciki na babu, idan akwai ayi dai-dai karfi idan kuma babu a hakura.
Sunana Hafsat Yusuf daga Karamar Hukumar Isa A Jihar Sokoto:
Yanayi baya hana mutane tattali da shiri domin watan Ramadan, sauki a wurin Allah yake. Al’adar Ramadan basket za ta yi kasa sosai, saboda dawainiyar za ta yi nauyi sosai duba da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa, babu amfani ga yin ramadan basket saboda wasu mutanen sukan yi abun da ya fi karfinsu saboda a yabe su, daga karshe ina ba ‘yan uwa shawarar kulawa da ibadun watan Ramadan da kuma yawan yin istigfari.
Sunana Sa’idu Suleman Malam Madori A Jihar Jigawa:
To a takaice dai na yi shiri na watan Ramadan wajen koyi da fiyayyen halitta da dukufa wajen bautawa mahalicci domin neman ‘yantuwa a wajen Ubangiji. ‘Yanmata sun yi shiri tsaf domin amsar Ramadan basket kamar yadda suke fada yayin da samari suma sun shirya wajen bayarwa duk da dai yanayin matsi da karancin kudade a hanun al’ummah. Haka magidanta suna shirye-shirye domin kyautatawa ga iyalansu, makomar ramadan basket a takaice dole ta canja zani ba kamar baya ba duba da yanayin rayuwa da tattalin arziki, Suma mata dole su yi hakuri da yadda suka samu. To amfanin ramadan basket bai wuce kara dankon soyayya a tsakanin samari da ‘yanmata ba musamman a wannan yanayi da ake ciki, hakan kyautatawa ne kwarai.
Sunana Alh Ahmad Salisu daga Karamar Hukumar Isa, Jihar Sokoto:
Mun shirya tsaf domin zuwan azumin watan Ramadan da abubuwa daban-daban, ramadan basket yanada kyau idan saurayi ya kyautatawa budurwanshi da ababuwan mure rayuwa. Shawarata ga al’umma ita ce mu yawaita karatun Al-kur’an da azkar da sadaka.
Sunana Usman Adamu Malam Madori A Jihar Jigawa:
Shirye-shiryen da ake yi ba kamar irin na lokacin daya shude ba, domin lokacin daya shude a saukake ake yin shirin amma yanzu ana fama sosai Allah ya dafa mana Amin. ramadan basket yana da matukar mahimmaci a tsakanin masoya ko kuma bestie saboda yana kara dankon mu’amala ta kasantuwar juna. Sai dai kuma mun tsici kanmu a wani irin yanayi na tsananin tsadar rayuwa wanda ba kowa bane zai iya yin wannan hidimar ta ramadan basket a wannan lokacin bisa yanayin aljihunan samarin sun yi low mata a yi hakuri.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano LGA Jihar Kano:
Niyyar ibada da kara kaimi wajen addu o i domin samun saukin wannan kuncin rayuwar da muke ciki. Gaskiya babu wani tasiri da zai yi duba da yanzu koda kasuwanci ka ke yi abin yayi baya (ciniki) sannan kuma ga tsadar kayyakin da ake yi domin gabatar da wannan kyauta din.
Sunana Muh’d Uba:
Gaskya idan muka duba abin da addini ya shawarci al’umma game da almubazarancin dukiya, sannan duba ga halin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp