Masu karatu barkanmu da war haka. Yau Alƙalaminmu karkata ya yi zuwa wani ɓangare mai mahimmanci a rayuwar ‘yan ƙasa, wanda idan ya faɗi ko ya samu tangarɗa, rayuwar masu rauni, da masu ƙaramin ƙarfi musamman mafi yawancin ‘yan ƙasa, tana cikin barazana.
Wannann ɓangare, shi ne gatan talaka, gatan wanda aka danne ko aka tauye wa hakki, wato ɓangaren Shari’a.
Ɓangaren Shari’a, yana ɗaya daga cikin ginshiƙan gwamnati Uku, da suka haɗa da ɓangarorin Zartarwa da Dokoki.
Ɓangaren Shari’a a Nijeriya, yana da alhakin bayyana dokoki, kare kundin tsarin mulki, da kuma tabbatar da adalci. An tsara tsarin shari’a a karkashin jagorancin Kotun Ƙoli inda Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ke kula da ita, sannan Kotun Ɗaukaka Ƙara da Manyan Kotuna a matakin jiha da tarayya.
Daga cikin manyan haƙƙoƙin da suka rataya akan ɓangaren Shari’a, akwai fassara kundin tsarin mulki da dokoki don amfani da su a shari’o’i. Sulhunta masu saɓani da kare haƙƙin ‘yan ƙasa da kuma tabbatar da cewa, sauran sassan gwamnati suna aiki a cikin iyakokin kundin tsarin mulki.
Amma, mu tambayi kanmu, wai me ke faruwa a ɓangaren Shari’a, ake samun hukuncin Shari’a ɗaya masu karo da juna?
An samu ruɗani a Kano a ranar Talata, 29 ga Mayu, 2024 bayan wani umarnin kotu guda biyu masu karo da juna game da taƙaddamar da ta taso kan sarautar Masarautar Kano tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi na II da Aminu Ado Bayero, sarkin da aka sauke.
Yayin da Mai Shari’a S. Amobeda na Babbar Kotun Tarayya, Kano, ya umarci Sufeto Janar na ‘Yansanda, Kayode Egbetokun, da Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kano, Hussain Gumel, da su tabbatar da cewa, an bai wa Aminu Ado Bayero dukkan haƙƙoƙin gata da ake bai wa sarakuna, nan take kuma, Mai Shari’a Amina Aliyu ta Babbar Kotun Jihar Kano ta hana ‘yansanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), da Sojojin Nijeriya korar Muhammadu Sanusi na II, Sarkin Kano da aka dawo da shi kan kujerar sarautar.
Taƙaddamar dai ta fara ne a lokacin da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Bayero daga kan sarautar Masarautar Kano, tare da wasu Sarakuna huɗu na Rano, Bichi, Karaye da Gaya inda kuma ya mayar da Lamido Sanusi a matsayin Sarki bayan soke dokar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi amfani da ita wajen sauke shi daga kujerar mulki a shekarar 2020.
Da yake magana kan halin da ake ciki a Kano, wani lauya mazaunin Abuja, Kennedy Khanoba, yayin da yake tattaunawa da Jaridar PUNCH ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya bar doka ta yi aiki, a ajiye maganar siyasa a gefe, yanzu doka tana hannun gwamnan jihar.
Har ila yau, Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) ta nuna rashin jin daɗi game da hukunce-hukuncen da ke karo da juna daga kotuna.
Ƙungiyar lauyoyin ta yi wannan kira ne yayin da take yi wa ‘yan jarida bayani kafin Makon Shari’a na 2025, inda ta kuma yi kira da a yi gyare-gyare don daidaita shari’o’in kafin zaɓen dake tafe a ƙasar.
Sai dai, shugaban na NBA reshen Akure, ya yi karin haske da cewa, “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi. Yayin da wasu masu ruwa da tsaki a ɓangaren Shari’a ke zargin ke zargin ɓangaren zartarwa da tsoma baki a Shari’o’in da suke da wani ra’ayi na musamman akai.
To, ko meye ke haifar da wannan hukunce-hukuncen masu bugu da juna?













