Ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Philippines, ya fitar da wata sanarwa kwanan nan dake cewa, Amurka za ta samar da tallafin dala miliyan 8 ga Philippines, don taimaka wa kasar zamanantar da ayyukan rundunar masu tsaron gabobin teku.
Wata kila, wasu na ganin cewa, wannan ya kasance “alfanu” da Philippines ta samu daga wajen Amurka, sakamakon yadda ta taimaki kasar wajen rura wutar rikici a tekun kudancin kasar Sin, karkashin manufar Amurka da ta shafi tekun Indiya da na Pasifik. Amma hakikanin gaskiya, Philippines za ta dandana kudar ta daga wannan abu.
A hakika, Amurka ta dade tana bayar da kudin tallafi, da haifar da hadarin dake tattare da yake-yake, domin neman samun riba, wato tana amfani da kudi kadan don cimma babban muradi, al’amarin da ya kasance a fayyace ga kowa. Alal misali, a shekara ta 2023, Amurka ta sayar da makaman da darajarsu ta kai dala biliyan 238 ga sassan kasa da kasa, darajar da ba’a taba ganin irinta ba a tarihi. Amma abubuwan da Amurka ta haifar ga kasashe daban-daban, su ne tashe-tashen hankali gami da rikice-rikice. Yanzu Amurka ta sake daukar irin wannan mataki kan Philippines, inda ta ba ta riba kadan, da zummar kara tsunduma Philippines cikin rikicin tekun kudancin kasar Sin, da kara amfani da ita wajen rura wutar rikici, da tada kayar baya ga sauran kasashe, ita kanta kuma ta cimma muradunta. (Murtala Zhang)