Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari jiya Laraba a nan birnin Beijing, da wakilan bangarorin masana’antu da kasuwanci da ilimi na Amurka, wadanda suka kawo ziyara kasar Sin, al’amarin da ya ja hankalin kasa da kasa. A cewar shugaba Xi, matsayar da aka cimma mafi girma tsakaninsa da shugaban Amurka Joe Biden a wajen shawarwarin da suka yi a San Francisco a bara shi ne, a tabbatar da bunkasar dangantakar Sin da Amurka yadda ya kamata, da kara kyautata ta. Su ma a nasu bangaren, wakilan Amurka sun ce, “tarkon Thucydides” ba dole ne ya faru ba.
“Tarkon Thucydides” na nufin, dole ne wata sabuwar kasa dake tasowa, ta kalubalanci manyan kasashe masu ci gaba, su kuma kasashen masu ci gaba, dole za su dauki matakin taka birki ga ci gaban kasar dake tasowa, ke nan rikici har ma yaki ka iya tasowa tsakaninsu. Abun sha’awa a nan shi ne, wanda ya bullo da wannan ra’ayin na “tarkon Thucydides”, kana wanda ya kafa makarantar gwamnati ta John F. Kennedy dake jami’ar Harvard, Graham Allison, na daya daga cikin wakilan Amurka da suka halarci shawarwarin. To, mene ne dalilin da ya sa wakilan Amurka suka ce ba dole ne “tarkon Thucydides” ya faru ba?
- Zhao Leji: Zuba Jari A Sin Zuba Jari Ne Don Gaba
- CMG Ya Kaddamar Da Wasu Sabbin Shirye-Shiryen Bidiyo Masu Amfani Da Fasahar AI
Na farko, nasarorin da Sin da Amurka suka cimma, damarmaki ne ga juna, al’amarin da aka riga aka tabbatar da shi sau da dama. Hakikanin gaskiya, daga cikin wakilan bangarorin masana’antu da kasuwanci na Amurka da suka halarci shawarwarin a wannan karo, akwai da yawa da suka ci gajiya daga hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fannin tattalin arziki da kasuwanci.
“Tarkon Thucydides” ba dole ne ya faru ba, magana ce dake kunshe da kyakkyawan fatan mutanen bangarorin masana’antu da kasuwanci da ilimi na Amurka ga shugabannin kasarsu, wato su fahimci kasar Sin yadda ya kamata. Idan an waiwayi dangantakar Sin da Amurka a ‘yan shekarun nan, babban abu shi ne Amurka na mayar da kasar Sin a matsayin babbar aminiyar hamayyarta bisa manyan tsare-tsare.
Haka zalika, “tarkon Thucydides” ba dole ne ya faru ba, saboda mu’amala da zumuncin dake tsakanin al’ummun Sin da Amurka.
A bana ne ake cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka. A halin yanzu, ana kara samun muradu iri daya tsakanin kasashen biyu. “Tarkon Thucydides” ba dole ne ya faru ba, ra’ayi ne daya da aka cimma tsakanin mutanen bangarorin masana’antu da kasuwanci da ilimi na Amurka, wanda kuma ya kamata ya kasance ra’ayi daya da aka cimma tsakanin shugabannin kasar. (Murtala Zhang)