Malam mene ne hukuncin tsayar da gemu shin wajibi ne ko mustahabbi, sannan aske shi haramun ne ko makaruhi?
To dan uwa Annabi (SAW) yana cewa: Ku saba wa mushrikai, ku cika gemu, ku rage gashin baki, kamar yadda ya zo a hadisin Bukhari mai lamba ta : 5553 da kuma Muslim a lamba ta: 259.
- Firaministan Pakistan Ya Gode Wa Sin Bisa Taimakon Da Ta Baiwa Kasarsa Wajen Yaki Da Ambaliyar Ruwa
- Gwamnatin Kano Ta Amince A Rushe Gine-Ginen Da Suka Haddasa Ambaliyar Ruwa A Kantin Kwari
Wannan ya sa da yawa daga cikin malamai suka tafi a kan wajabcin tsayar da gemu da kuma haramcin aske shi, har ma wasu malaman kamar Ibnu Hazm sun hakaito ijma’in malamai a kan haka, kamar yadda ya zo a littafinsa na maratibul ijma’i shafi na: 157.
Malamai suna cewa har abin da aka rawaito daga wasu sahabbai kamar Ibnu Umar cewa suna rage gemu idan ya kai wani geji, to suna yi ne lokacin hajji saboda suna ganin hakan na daga cikin rage kazantar da alhaji yakan yi bayan ya gama aikin hajjinsa.
Sannan gemu na daga cikin abubuwan da ke kara wa namiji kwarjini da kyau, shi ya sa za ka ga wanda yake aske shi yana kama da tsohuwar da kyanta ya disashe, kamar yadda Sa’adi ya fadi a Bahjatu kulubul abrar shafi na: 50.
Sai dai malamai suna cewa idan mutum yana garin da za a iya kashe shi idan ya bar gemunsa, to zai iya askewa saboda lalura, sai dai ya wajaba kowacce lalura kar ta wuce gwargwadonta. Don neman karin bayani duba littafin : Wujubu I’ifa’ul liha .
Allah ne mafi sani