Malam idan ana binka ramuwar azimi za ka iya niyya biyu, wato da nufin sittu shawwal da kuma ramuwar Ramadhana a lokaci guda ? Don Allah malam taimaka min da bayani.
To ‘yar’uwa kowanne daban ake yinsa, saboda manufarsu ta bambanta, don haka ba za’a hada su da niyya daya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma’a, za mu fahimci hakan a cikin fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : “Duk wanda ya azumci Ramadhana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara” Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu- shawwal daban.
Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal” ya sa wasu malaman sun tafi akan cewa : bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan, kamar yadda ya zo a: sharhurmumti’i 6\443.
Allah ne mafi sani.