Ranar 1 ga watan Yuli ne aka cika shekaru 102 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin wato JKS. A daidai lokacin da ake bikin wannan rana, babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, shugaban kasa, kana, shugaban kwamitin soja na kasar Sin, Xi Jinping ya bukaci a warware matsalar musamman dake gaban jam’iyyar, da kyautata tsarin gudanarwar harkokin jam’iyyar daga dukkan fannoni, da kara kwarewar aikin jami’an kasar, ta yadda za su ba da gudummawa wajen farfado da al’ummar Sinawa baki daya. Mene ne ma’anar sakon da Xi Jinping ya bayar, kuma mene ne alakar mulkin jam’iyya da na kasa?
Duk wanda ya fahimci tarihin kasar Sin ya san cewa, tarihin kasar Sin cikin shekaru 100 da suka gabata, ba a iya raba shi da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ba, kuma tasowa ko faduwar kasar yana da alaka da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A cikin shekaru 100 da suka gabata, nasarar da JKS ta samu ya dogara ne kan jagoranci mai karfi, raya kanta, da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
A halin yanzu, Xi na ci gaba da jagorantar aikin yin kwaskwarima ga JKS, ya kuma tsaya tsayin daka wajen gudanar da ayyukan JKS bisa tsari, da yin kwaskwarima, domin warware matsala ta musamman dake gaban wannan babbar jam’iyya a duniya, ta yadda jam’iyyar za ta ci gaba da ba da jagoranci ga kasar Sin, a kokarin wadatar da al’ummar ta, da neman farfadowar kasar Sin, gami da shimfida zaman lafiya mai dorewa, da tabbatar da jin dadin al’umomin duniya baki daya.
Xi Jinping na mai da matukar hankali kan gudanarwar harkokin JKS, inda ya bukaci a gudanar da harkokin JKS kamar yadda aka tsara a dukkan fannoni, kuma, ya hada wannan bukata tare da aikin gina kasa mai tsarin gurguzu ta zamani a dukkan fannoni, da zurfafa aikin kwaskwarima a dukkan fannoni, da gudanar da ayyukan kasa bisa doka a dukkan fannoni, wadanda suka kasance babbar manufa da babban tsarin gudanar da harkokin kasar Sin, lamarin da ya nuna dangantakar dake tsakanin JKS da aikin zamanintar da kasa, wayewar kan kasa, farfadowar kasa. Ma’ana, bin jagorancin JKS shi ne tushen gudanar da harkokin kasa kamar yadda ake fata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)