• English
  • Business News
Saturday, October 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mene Ne Tsarin 5G?

by Ibrahim Sabo
2 years ago
5G

Tsarin 5G wani tsari ne na intanet da ke bayar da damar saukewa da dora sakonni cikin matukar sauri a intanet.

Yana bai wa wayoyi da sauran na’urori da yawa damar amfani da intanet a lokaci guda.

  • Yawan Sinawa Masu Amfani Da Intanet Ya Kai Fiye Da Biliyan 1
  • An Kaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana’o’i A Kano

“Duk abin da muke yi da wayoyinmu yanzu, za mu iya yi da tsarin 5G amma cikin sauri kuma cikin sauki,” a cewar Ian Fogg na OpenSignal, wani kamfanin waya.

Ku yi tunanin tarin jirage marasa matuki sun hada kai wajen gudanar da aikin bincike da ceto da sa ido kan tarin motoci da ke wuri guda, kuma duk suna aiki tare suna sadar da bayanai ga juna ba tare da amfani da waya ba, kuma dukansu suna amfani ne da tsarin 3G.

Haka kuma, mutane da yawa na ganin cewa tsarin 5G zai taka muhimmiyar rawa kan abubuwan hawa maras matuka wajen musayar bayanai a tsakaninsu.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

Yaya tsarin yake aiki?

Wata sabuwar fasaha ce, amma idan aka fara amfani da ita ba lallai ne a fahimci saurin intanet din ba saboda akwai yiwuwar amfani da tsarin 5G ne daga farko wurin inganta tsarin 4G.

Saurin da wayarka za ta yi zai danganta ne da kamfanin sadarwarka da yadda suke amfani da tsarin 5G da kuma irin kayan aikinsu.

Saurin tsarin 4G a halin yanzu na bayar da gudun 45Mbps (duk dakika daya). Amma ana sa rai tsarin 5G na iya samar da sauri sau 10 zuwa 20 fiye da na 4G. Wannan zai ba da damar sauke fim, wato ‘downloading’, cikin minti guda.

Ci gaban da za a samu a sauri da ingancin intanet zai fara aiki ne idan kamfanonin sadarwar suka kafa tsarin 5G mai zaman kansa, inda duka ayyukansu na amfani da fasahar 5G.

Me ya sa za mu bukaci tsarin?

Kusan duka al’amuran duniya sun dogara ne kan wayoyin hannu kuma amfani da data na karuwa duk shekara, musamman wajen kallon bidiyo ke karuwa.

Tsare-tsaren da ake da su yanzu suna kara takurewa, shi ya sa ake samun cunkoso ko tsaiko a network musamman idan akwai mutane da yawa a wuri guda suna kokarin amfani da network guda a lokaci guda.

Tsarin 5G ya fi saukin bai wa dubban na’urori damar amfani da network guda a lokaci guda, kama daga wayoyin hannu zuwa na’urar daukar hoto da fitilun kan titi masu kunnawa da kashe kansu.

Zan bukaci sabuwar waya kafin na iya amfani da tsarin?

Eh. Amma a lokacin da aka kaddamar da tsarin 4G a shekarar 2009 zuwa 2010, a daidai lokacin ne aka fara sayar da sabbin wayoyi.

Kuma mutane sun yi ta korafin cewa kudin data ya karu yayin da ingancin networ din bai gyaru ba.

Tsarin zai yi aiki a karkara?

Ana yawan korafi kan rashin network mai karfi a yankunan karkara. Amma tsarin 5G ba lallai ne ya yi maganin wannan korafin ba.

Tsarin 5G zai fi aiki ne a birane da ke da yawan mutane.

Kamfanonin sadarwa za su fi mayar da hankali ne kan inganta tsarin 4G LTE a yankunan da ke wajen birane yayin da suke kaddamar da 5G a biranen.

Amma wannan na nufin, ga mutanen da ke kauyuka, ingancin network dinsu ba zai gyaru ba har sai gwamnati ta sa manufofin da za su taimaki kamfanonin sadarwa yadda za su ji dadin kafa karafunan sadarwa a karkara.

Mun nakalto muku ne daga shafin BBC Hausa

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai
Da ɗumi-ɗuminsa

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

September 5, 2025
Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

April 19, 2025
Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet

March 8, 2025
Next Post
Ba Mu Hana Sulhu Da ‘Yan Ta’adda Ba, Amma A Bar Jami’an Tsaro Su Yi Aikinsu – Bosso

Ba Mu Hana Sulhu Da 'Yan Ta'adda Ba, Amma A Bar Jami'an Tsaro Su Yi Aikinsu - Bosso

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba

Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba

October 11, 2025
Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara

Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara

October 11, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta

October 11, 2025
Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

October 11, 2025
Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

October 11, 2025
Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

October 11, 2025
Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

October 11, 2025
sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida

October 11, 2025
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.