Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa wanda ke buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami kuma tsohon ɗan ƙwallon FC Barcelona Lionel Andre Messi ya sake karya wani tarihi a Duniyar ƙwallon ƙafa bayan ya lashe kofin Copa America da aka kammala a katsar Amurka.
Da wannan ne Messi mai shekaru 38 ya lashe kofuna 45 jimilla a tarihin kwallon kafa da ya shafe shekaru 20 yana yi,wanda kuma hakan yasa ya zama ɗan wasan da yafi lashe yawan kofuna a tarihi.
- Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa
- 30 Watan Oktoba 2023: Messi Ya Lashe Gasar Ballon d’ Or
Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na Balloon d’or sau 8 jimilla,ya jagoranci ƙasar Ajantina domin lashe wannan kofi na bana wanda kuma shi ne na 3 da ƙasar ta lashe a ƙasa da shekaru huɗu.
Yanzu Messi ya karya tarihin da tsohon abokin wasansa a FC Barcelona Dani Alves ya kafa na dan wasan da yafi lashe kofuna a tarihin ƙwallon ƙafa.