Ana sa ran Lionel Messi zai lashe kyautar Ballon d’Or karo na takwas a cikin wannan watan bayan da aka fitar da jerin sunayen wadanda za su lashe kyautar maza da mata na 2023.
Wannan dai na zuwa ne bayan dan wasan mai shekaru 36 ya samu daukaka da Argentina bayan da ya jagorance ta zuwa gasar cin kofin duniya da aka yi a Katar a bara kuma ta lashe kofin.
- Argentina Ta Gayyaci Messi Buga Mata Wasa Duk Da Raunin Da Ya Samu
- Shirin Bunƙasa Ilmi A Kano: Yadda Gwamnatin Abba Gida-gida Ta Tura Dalibai 1001 Karatu Kasashen Waje
Tsohon dan wasan na Barcelona da Paris Saint-Germain daga nan ya koma Inter Miami a watan Yuli kuma nan da nan ya baje kolin iyawarsa a kungiyar dake buga gasar MLS.
A cewar kafar yada labarai ta DIARO SPORT ta Spaniya, Messi za a ba shi kyautar Ballon d’Or karo na 8 a gaban Erling Haaland na Manchester City, wanda ya taimaka wa kulob dinsa da ya lashe kofin UEFA Champions League.
Da Kylian Mbappe wanda ya lashe kyautar takalmin zinare a gasar cin kofin duniya da aka kammala.
Mbappe ya jagoranci Faransa zuwa wasan karshe a Katar, inda ya zura kwallaye uku a ragar Argentina, sai dai sun sha kashi a bugun fenariti.
Baya ga nasarar da Messi ya samu, rahoton ya kara da cewa ‘yar wasan tsakiya ta Barcelona Aitana Bonmati za ta lashe kyautar Ballon d’Or ta mata a karon farko bayan nasarar da Spaniya ta samu a gasar cin kofin duniya ta mata.
Kamar yadda ya faru da Messi, Bonmati kuma ta lashe kyautar zinare a gasar cin kofin duniya ta mata ta bana, kuma ‘yar shekaru 25 din ta lashe gasar zakarun Turai da gasar Laigar mata da La Blaugrana.