Shahararren dan kwallon kafar duniya Lionel Messi, ya amince ya koma kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke buga gasar Major League Soccer ta kasar Amurka bayan da zamansa a PSG ya zo karshe.
Messi ya bayyana cewar ya zabi komawa Amurka ne saboda ya samu sabuwar rayuwa kuma ba ya son ya komawa kungiyar Barcelona saboda baya son ya kara tsintar kansa a irin yanayin da ya tsinci kansa a lokacin da zai bar kungiyar a 2021.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Alkali A Adamawa
- Yau Za A Yi Jana’izar Tsohon Wazirin Kano, Sheikh Nasir Muhammad Nasir
“Bana son na sake fama ciwon da ke raina kuma bana bukatar na zama silar korar wani ko wasu a kungiyar domin na ji cewar in har Barcelona za ta iya dawo da ni dole sai an kori wasu ko kuma a rage wa wasu albashin da su ke karba wanda ni ba zan so na zama sila ba,” in ji Messi.
Messi wanda ya shafe shekaru 21 a Barcelona ya jefa kwallo 672, inda ya lashe kofuna da dama ciki har da Laliga guda 10, gasar zakarun turai huru da kuma Spanish Super Cup 7.
An danganta komawarsa Al-Hilal ta kasar Saudiyya, amma ya ce shi ba kudi yake yi wa kwallo ba kawai yana yi ne don sha’awa da kuma iyalinsa.
Messi ya lashe gasar Ligue 1 ta kasar Faransa har sau biyu, inda a kakar bana ya jefa kwallaye 16 kuma ya taimaka aka jefa 16.
Zamansa a kungiyar ta Faransa ya zo karshe bayan kammala kakar bana, inda ya yanke shawarar komawa Inter Miami da ke mataki na 15 a gasar MLS ta kasar Amurka.