Jami’ar Bayero ta Kano, (BUK)ta samu wani gaggarumin ci gaba wajen karawa miji da mata girma zuwa mukamin Farfesa Suleiman Mainasara Yar’adua da Aisha Haruna, da suka yi wa zuwa mukamin. Wannan samun ci gaban an same shi ne bayan auren da suka yi wanda ya shafe shekara 24 da kuma aiki tukurun da suka yi wa ita jami’ar.
Ma’auratan irin ci gaban da suka rika samu da karin girma wata manuniya ce ga aiki tukuru wanda suke yi, mai da hankali, da kuma jajircewa da ayyukansu na koyarwa a jami’ar.Shi dai Farfesa Yar’adua, mai fada aji ne kan lamarin daya shafi ci gaban harkar sadarwa,ya bada muhimmiyar gudunmawa ta vangaren ta hanyar bincke wallafe- wallafe.
- Jami’ar Bayero Ta Fito Da Kurakuran Da Ake Tafkawa A Rediyo Da Talabijin
- Binciken Jami’ar Bayero Ya Gano A Hoton Yatsa Za A Iya Gane Mai Cutar Daji – Farfesa Darma
Matar shi, Farfesa Aisha Haruna, wata shahararriya ce kan aikin lauyan da ya shafi al’umma,ta bunkasa shi sashen nata ta hanyar maida hankali kan lamarin daya shafi hakkin dan Adam da kuma lamarin daya shafi zamantakewa,siyasa da al’adun da suka shafi yadda al’umma suka sauya.
Ci gaban nasu ba kawai ya tsaya a jami’ar bane har ma da sauran al’umma da harkokin su suka shafi lamarin koyarwa a jami’a.Tunawa da ayyukan da suka yi ya nuna ana sane da duk abubuwan da suka yi lokaci ne na yin abin da ya kasance yanzu.
Farfesa Yar’adua da Farfesa Aisha Haruna sun nuna jin dadinsu ga karin girman da aka yi masu na mukamin Farfesa, yin hakan ya nuna suna da kudurin ci gaban dukkan vangarorin karatun da kowa yafi kwarewa, ta kuma taimakawaci gaban jami’ar.
Sun bayyana cewa “daga su zuwa mukamim Farfesa hakan zai basu kwarin gwiwa su mai da hankalinsu kan ci gaban jami’ar,” sun bayyana hakan ne a kafar sadarwa ta mujallar jami’ar mai suna the BUK Bulletin. Al’ummar jami’ar sun taya mijin da matar, inda suka nuna irin jin dadin da suka yi dangane aiki tukuru da hadin gwiwarsu a matsayin wata manuniya ce ga samun nasarar harkokin koyarwar ta. Ci gaban da suka samu ya nuna sun sa hakuri da kuma lamarin tuntuvar wasu kafin, a kai ga cimma shi muradin.
Da suka kasance suna mutane na farko a matsayin miji da mata a lokacin da ake ciki wadanda suka kai ga samun mukamin Farfesa a duk a rana daya a jami’ar Bayero, ita sa’ar ta su ta kasance a matsayin wani abin alfahari ga abokan aikinsu da kum dalibai.