‘Yansanda a Jihar Legas sun cafke wani magidanci mai shekara 49, mai suna Lawrence Itape, da ke zaune a yankin Ajah bisa zargin kashe matarasa ta hanyar daba mata wuka.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce, Lawrence, ya kashe mai dakinsan ne, saboda cacar bakin da ta kaure a tsakaninsu a kan karancin ruwan sha a sashen rukunin gidajen da suke haya.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa A Tsakanin Kafofin Watsa Labaru Na Sin Da Na Kasashen Larabawa
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa A Tsakanin Kafofin Watsa Labaru Na Sin Da Na Kasashen Larabawa
Benjamin ya ce, bayan an kawo rahoton aukuwar lamarin, DPO mai kula da caji ofis na yankin Langbasa, Stephen Abolarin, ya tura Jami’ansa zuwa inda lamarin ya auku, inda suka kamo Lawrence tare da kwato wukar da ya yi amfani da ita wajen aikata ta’asar.
A cewar Benjamin, an tura maganar da kuma Lawrence zuwa ga sashen gudanar da bincike na SCIID da ke a yankin Panti, Yaba a jihar don a gudanar da dogon bincike.
Ya ce, an kai gawar matar zuwa dakin ajiye gawarwaki na babban asibitin Mainland da ke a Yaba don yin gwaji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp