Wani abu da ba’a saba gani ba mai kama da abin mamaki shi ne, wani dan kasuwa mai suna Nasiru Yunusa ya nemi matarsa Aisha Hamisu ta biya shi Naira miliyan 1 sannan ya sake ta.
Ma’auratan, wadanda suka yi aure a karkashin tsarin shari’ar Musulunci a shekarar 2021, suna ‘ya mace mai watanni 13 da haihuwa, sun shiga zazzafan rikicin da ya kai ga neman rabuwa, kafin lamarin ya kai su gaban Kotu dake Kubwa dake Babban Birnin Tarayya.
- ’Yan Sama Jannati Na Kumbon Shenzhou-17 Sun Gama Aiki A Wajen Kumbo A Karon Farko
- Kamfanin Man Nijeriya Ya Sa Hannu Kan Fasahar Gano Sinadarin Methane
Aisha ta danganta wannan rabuwar tasu ga nuna rashin kulawa da mutunta ta da mai gidan nata baya da cewa su ne musabbabin neman a raba aurensu, ta bayyana cewa Yunusa ya kore ta daga gidansa ne a watan Afrilun 2022, inda ya tilasta mata komawa gidan iyayenta tare da ’yarsu.
Duk da haka, Yunusa ya nuna sha’awar yin sulhu ta hanyar biyansa kudi masu kauri, ya yi ikirarin ya kashe Naira miliyan 1 kan kudaden lauya da kuma wasu kudade da suka shafi shari’ar da ake yi a kotu, ya bukaci ta biya shi wannan kudi ne a matsayin diyyar saki.
“Ina da shaidar na kashe Naira miliyan 1,” Yunusa ya bayyana a kotu.
Nan take Aisha Hamisu ta yi fatali da wannan bukata tasa, ta kuma musanta duk wani sha’awar soyayya ga Yunusa, kuma ta nuna sha’awarta ta kawo karshen auren. Bugu da kari, ta musanta samun tallafin kudi daga gare shi, inda ta nuna cewa ta ita ta dauki nauyin kashe kudin haihuwar ‘yarsu wacce sai da aka yi mata aiki asibiti aka cire ta a sashen ‘C-section surgery’.
“Na yarda in mayar masa da sadakin da ya bani Naira 50,000, shi ke nan,” in ji ta a matsayin abin da Yunusa ya bukata.
Alkalin kotun, Mista Mohammed Wakili, ya dage