Mai girma ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari da gwamna Nasir Idris sun kaddamar da shirin bunkasa noma mai taken KADAGE a Karamar Hukumar Suru da ke Jihar Kebbi.
A shirin an raba famfunan ruwa masu amfani da hasken rana da injinan wutar lantarki ga manoma a karkashin shirin bunkasa noma da ci gaban mai taken KADAGE.
- Kafofin Yada Labarai Na Yamma Bayin Kudi Ne
- Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Wa Sarakuna Bada Izinin Hakar Ma’adanai
A cewar ministan, Shugaba Bola Tinubu, ya himmatu wajen inganta harkar noma da kuma samar da wadataccen abinci a kasar nan daidai da ajanda takwas na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
“Shugaba Tinubu ya sanya batun samar da abinci na daya a cikin ajandarsa takwas ta hanyar inganta noma a kasar nan.
“Dukkan shirye-shiryen da ke cikin ajandar na da alaka da noma, kamar samar da arziki da kawar da fatara da bunkasa tattalin arziki.
“Shugaban kasa ya damu da yadda manoma za su iya samun kayan aikin noma kuma a yanzu ya fara wani tsari na hanzarta samar da irin wadannan kayan amfanin gona ga manoma,” in ji shi.
Sanata Kyari, ya sanar da taron cewa Gwamna Nasir Idris ya kai ziyara a ofishinsa da ke Abuja domin tattauna hanyoyin inganta noma a jihar.
“Ta hanyar ayyukan Gwamna Idris, ya ‘tattaki zance’ ta hanyar sayo da raba famfunan ruwa masu amfani da hasken rana guda 6,000 da sauran kayan aiki don bunkasa noman ban ruwa a jihar,” in ji shi.
Ministan ya lura cewa noman a duk shekara zai bunkasa noman amfanin gona, da kara samar da ayyukan yi, da rage fatara, da rage hauhawar farashin abinci da kuma kara hada kai.
“Wadannan manufofi ne da aka bayyana a cikin Shirin Sabunta Fata na Shugaba Tinubu. Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin da aka zaba domin noman rani,” inji shi.
Ya yaba wa gwamnan bisa goyon bayan da ya bayar bisa ga kiran da shugaba Tinubu ya yi na hada hannu tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi domin tabbatar da samar da kayayyakin noma ga manoma domin a samu nasarar samar da isasshen abinci.
Da yake raba kayan amfanin gonan, gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya ce gwamnatinsa za ta raba famfunan ruwa masu amfani da hasken rana guda 12,000, inda za a fara raba 6,000 ga manoma domin su kara yawan amfanin gona.
“Gwamnatin jihar za ta sayo raka’a 20,000 na famfunan iskar Gas (CNG) masu amfani da ruwan famfo a matsayin tallafi ga fanfuna masu amfani da hasken rana domin kara yawan manoman da za su amfana a jihar,” in ji shi.
Dokta Nasir ya gargadi wadanda suka amfana da kada su sayar da kayayyakin, inda ya ce gwamnati za ta dauki matakin ladabtarwa a kan duk wanda aka samu yana sayar da famfon da aka bashi don aikin bunkasa noma a jihar, in ji shi.
“Na rantse da Allah duk wani jami’in gwamnati da ke da hannu wajen rabon kayayyakin da aka samu da hannu wajen karkatar da su, za a kama shi kuma a hukunta shi.
“Na umarci dukkan shugabannin hukumomin tsaro da suka hada da kungiyoyin ‘yan banga da su sanya ido a kan yadda ake raba kayayyakin tare da daukar matakin da ya dace kan masu karya doka,” in ji shi.
Ya kuma kara da bayyyana cewa magabacinsa, Sen. Atiku Bagudu, ya yi iya kokarinsa wajen sanya jihar a taswirar duniya a matsayin sa na kan gaba wajen noman shinkafa a kasar nan.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa zai karfafa aikin da aka samu tare da inganta noman noman.