Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan jarida da su guji tallata ’yan ta’adda da ‘yan bindiga da sauran miyagu da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasar nan.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin zama na bakwai na Jerin Zauren Bayanai na Ministoci na shekarar 2025 wanda aka gudanar a Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da ke Abuja.
- Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista
- Almundahana: LP Ta Nada Sanata Ireti Kingibe Domin Binciken Tsohon Shugaban Jam’iyyar
Idris ya ce, “Kafofin yaɗa labarai, a matsayin su na masu tantance labarai kuma abokan hulɗa wajen gina ƙasa, suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ƙarfafa gwiwar dakarun mu ta hanyar nuna irin nasarorin da suka samu da sadaukarwar da suke yi.
“Dole ne mu guji tallata waɗannan ƙungiyoyi. Dole ne mu cire su daga shafukan farko na jaridu, mu riƙa bayar da rahoto a kan su daidai da yadda suke — wato masu laifi ne — ba tare da ƙawata ayyukan su ko ba da muhimmanci ga ƙarya da farfagandar da suke yaɗawa ba.”
Ministan ya ƙara da cewa ‘yan ta’adda da sauran miyagun ƙungiyoyi suna amfani da kafafen watsa labarai da na sada zumunta ne domin su yaɗa fargaba da ƙarya da kuma jawo mutane zuwa gare su.
Saboda haka, ya buƙaci ’yan jarida da editoci da su zama masu kishin ƙasa da ƙwarewa wajen bayar da rahoto, ta hanyar guje wa manyan kanun labarai masu tayar da hankali da kuma ƙin zama hanyar yaɗa farfaganda ta masu aikata ta’addanci.
Ya ce: “Waɗannan ba ‘yan gwagwarmayar ‘yanci ba ne; masu kisa ne, masu sace mutane ne, masu ɓarna ne, kuma dole ne a bayyana su a hakan.”
Ministan ya kuma haskaka wani muhimmin ɓangare na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, musamman ɓangaren da ya shafi “Ƙarfafa Tsaron Ƙasa Don Samar Da Zaman Lafiya Da Cigaba.”
Ya ce Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da kashe kuɗi wajen samar da kayan aiki na zamani ga sojoji, da inganta binciken leƙen asiri da kuma haɓaka haɗin gwiwa da ƙasashen duniya.
Idris ya bayyana cewa Jerin Zauren Bayanai na Ministocin wani shiri ne da ma’aikatar sa ta ƙirƙira domin bai wa ministoci dama su faɗa wa ’yan Nijeriya irin nasarorin da suke samu, da ayyukan da ke gudana da kuma tsare-tsaren da za su aiwatar a nan gaba.
Ya ce, “Ta wannan dandali na tattaunawa, wanda ake watsawa kai-tsaye a tashoshin talbijin na ƙasa da kuma kafafen sada zumunta, muna ci gaba da nuna jajircewar mu ga gaskiya, ɗaukar nauyi, da haɗin kai da jama’a.”
Ministan ya yaba wa kafafen yaɗa labarai bisa goyon bayan da suke ba wannan shiri da kuma rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma game da ayyukan gwamnati.
A taron, Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, da Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Abbas, sun gabatar da bayanai ga manema labarai kan nasarorin da ma’aikatun su suke samu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp