Ministan Ilimi, Dr. Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana goyon bayansa ga ƙarin shekara guda ga tsarin aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC), daga shekara guda zuwa shekaru biyu, tare da faɗaɗa shirin koyon kwarewa da horon ci gaban kasuwanci na matasan.
A yayin ziyarar Daraktan NYSC, Brigediya Janar Olakunle Nafiu, a ofishin Ministan, Alausa ya kuma ba da shawarar a tura ƙarin malamai masu digiri zuwa makarantun karkara, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen cike ma’aikatan da ke cikin makarantun da ke yankunan karkara.
- Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga
- Bayan Kwana 22, Tsohon Shugaban NYSC Tsiga Ya Kuɓuta A Hannun Ƴan Bindiga
Ministan ya yaba wa NYSC kan ƙoƙarinsa na daƙile harkallar takardun shaida, musamman tsakanin ‘yan Nijeriya da suka yi karatu a ƙasashen yammacin Afirka, tare da jaddada cewa ana gudanar da binciken takardun masu digiri na ƙasashen waje.
Haka kuma, Alausa ya bayyana cewa ma’aikatar na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da ingantaccen tsarin duba takardun, yana mai cewa ma’aikatar da NYSC za su ƙara ƙarfafa haɗin gwuiwa wajen inganta ilimi domin ci gaban ƙasa.
A nasa jawabin, Brigediya Janar Nafiu ya yabawa sabbin ƙirƙire-ƙirƙiren da ma’aikatar Ilimi ta yi, musamman wajen inganta tsarin ilimi. Ya kuma ba da shawarar kafa wani rumbun bayanai na matasan Nijeriya da ke karatu a ƙasashen waje, wanda zai taimaka wa gwamnati wajen samun bayanan dalibai da kuma kawar da masu yin ƙaryar takardun shaida.
Mista Abel Olumuyiwa Enitan, Sakataren dindindin na ma’aikatar Ilimi, ya tabbatar da cewa ma’aikatar tana shirye don ƙara yin haɗin gwuiwa tare da NYSC domin inganta tsarin ilimi a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp