• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Ya Nemi ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Habaka Kasuwancin Iskar Gas Na CNG

bySulaiman
2 years ago
CNG

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su kasance kan gaba a shirin Gwamnatin Tarayya na yin amfani da Iskar Gas (CNG) a Nijeriya. 

Hadimin Musamman kan Yaɗa Labarai na ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, ya faɗa a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa, ministan ya furta haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin ƙaddamar da masana’antar iskar gas ta ABG CNG tare da yaye injiniyoyin 40 da su ka ƙware a harkar sarrafa CNG.

  • Jerin Jami’o’i 18 Da NUC Ta Haramta Karatu Acikinsu
  • Cire Tallafin Fetur: Kano Za Ta Biya Ma’aikata Karin Albashin N20,000, ‘Yan Fansho N15,000.

Idris ya ce wannan ƙoƙari da rukunin kamfanonin ABG Group ya yi abu ne wanda ya dace kuma ya zo a kan kari.

Haka kuma ya ce amfani da matsattsiyar iskar gas wani abu ne wanda ya zo kenan kuma shi ne hanyar rage kashe kuɗi a ɓangaren harkar sufuri.

Idris ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan yadda ya jagoranci yadda za a koma ana amfani da iskar gas ta CNG a maimakon man fetur a motocin haya da ƙanana na shiga.

LABARAI MASU NASABA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

Ya ce: “Iskar gas ta CNG ita ce za a riƙa amfani da ita nan gaba, don haka ya na da muhimmanci ga ‘yan kasuwa a Nijeriya su yi amfani da wannan damar ta shirin gwamnati kan CNG ɗin ta hanyar zuba jari na ɗaukar ma’aikata da sayen kayan aiki da ake buƙata don haɓaka sashen a duk faɗin Nijeriya.”

Ministan ya bayyana cewa ya zuwa yanzu har gwamnatin Tinubu ta kasafta naira biliyan 100 a matakin farko ga harkar gas ɗin CNG, kuma ma har ga shi Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi na’am da shirin CNG ɗin wanda hakan ya taimaka wajen sanyin da ta yi kan maganar da ke tsakanin ta da Gwamnatin Tarayya.

Shugaban rukunin kamfanonin ABG Group, Alhaji Bawa Garba, a nasa jawabin, ya ce amfani da iskar gas ta CNG wani maganin matsala ne salin alin wanda ya ke buƙatar goyon baya da ciniki daga gwamnati idan har ana so ya faɗaɗa har a riƙa yi wa Nijeriya kallon “Ƙasar Iskar Gas.”

CNG Ya ce: “Kamfanin mu ya na godiya ga Shugaba Tinubu saboda bajintar da ya yi wajen yanke shawarar a riƙa yin amfani da CNG. Mu da ma can kamfani ne wanda ke fara yin abu, don haka shaidar shigar mu cikin tsarin CNG ita ce yadda mu ka horas da ɗimbin injiniyoyin sauya CNG a faɗin Nijeriya.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Next Post
Taki

Zargin Sata: Jami’an ‘Yansanda A Kaduna Sun Kama Buhunan Taki Guda 600

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version