Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI) da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) bisa nasarar gudanar da zaɓukan sababbin shugabannin su.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan ya taya murna ga Musikilu Mojeed, shugaban kamfanin jaridar onlayin ta Premium Times, da Ahmed Shekarau, Manajan Daraktan kamfanin Media Trust, kan sake zaɓen su da aka yi a matsayin Shugaba da Sakatare, bi da bi, tare da wasu jami’ai huɗu da aka sake zaɓa.
- Kaduna: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Sayar Wa ‘Yan Jarida Buhun Shinkafa A Kan Naira 40,000
- Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Muhimmiyar Makalar Xi Mai Taken “Zurfafa Aiwatar Da Juyin Juya Halin Jam’iyyar Kwaminis Ta Sin”
Ya ce: “Ina taya Malam Musikilu Mojeed, Shugaban kamfanin Premium Times, da Ahmed Shekarau, Manajan Darakta na Media Trust, waɗanda aka sake zaɓen su a matsayin Shugaba da Sakatare, bi da bi, da kuma sake zaɓen wasu jami’ai guda huɗu na IPI reshen Nijeriya.”
Ministan ya kuma yaba wa sauyin shugabanci cikin lumana da ake yi a NUJ, wanda ya haifar da zaɓen Malam Alhassan Yahaya a matsayin Shugaba da kuma Abimbola Oyetunde a matsayin mace ta farko da ta zama Mataimakiyar Shugaban ƙungiyar ta ƙasa.
Har ila yau, Idris ya yaba wa gwamnatin Jihar Imo saboda rawar da ta taka wajen gudanar da zaɓen na NUJ.
Ya ce: “Dole ne in yaba wa gwamnatin Jihar Imo kan goyon bayan da ta bayar da kuma karimcin ta wajen karɓar baƙuncin membobi da wakilan NUJ, wanda ya taimaka wajen samun nasarar zaɓen.”
Daga nan ya yi kira ga IPI da NUJ da su ci gaba da jajircewa wajen inganta aikin jarida yadda ya dace.
Ya ce: “A matsayin ku na masu kare gaskiya, dole ne ‘yan jarida su ba da fifiko ga gaskiya da riƙon amana a cikin aikin su. Ina kira ga ƙungiyoyin biyu da su tabbatar da cewa membobin su suna bin mafi kyawun ƙa’idojin aikin jarida don inganta dimokiraɗiyyar mu.”
Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da kare ‘yancin ‘yan jarida, inda ya ce, “Za mu ci gaba da kare haƙƙoƙin ‘yan jarida, ta yadda za a tabbatar da yanayi mai kyau don aikin jarida ya bunƙasa a Nijeriya.”
Ita dai Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya, wato International Press Institute (IPI), wata ƙungiya ce ta duniya da ke ƙunshe da ‘yan jarida, editoci, da shugabannin kafafen yaɗa labarai da suka himmatu wajen kare ‘yancin ‘yan jarida da inganta aikin jarida mai zaman kan sa da bambancin kafafen yaɗa labarai a duniya baki ɗaya.