A jiya Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 cewa, babu maganar “rashin fahimta” ko “shubuha” idan ana batun Jamhuriyar Jama’ar Sin da ke wakiltar kasar Sin baki daya a MDD.
Da yake gabatar da jawabi yayin babban taron na MDD karo 79, Wang, ya shaidawa shugabannin kasashen duniya da suka halarci taron cewa, kasancewar Taiwan “wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba” batu ne na “tarihi kuma shi ne gaskiya.”
- Kasar Sin Ta Nuna Damuwa Kan Rikicin Isra’ila Da Lebanon
- Rawar Da Kasar Sin Ke Takawa Ta Fannin Sauya Fasalin Makamashi A Duniya
Sanarwar Alkahira da kuma sanarwar Potsdam sun bayyana karara cewa, dukkan yankunan da Japan ta sace daga kasar Sin, kamar Taiwan da tsibiran Penghu, za a mayar da su zuwa ga kasar Sin, kuma wannan ya zama wani muhimmin bangare na tsarin kasa da kasa bayan yakin.
“A nan, a wannan babban zauren, shekaru 53 da suka gabata, babban taron MDD karo na 26 ya amince da kuduri mai lamba 2758 da gagarumin rinjaye, inda aka yanke shawarar maido da dukkan ’yancin Jamhuriyar Jama’ar Sin a MDD, tare da amincewa da wakilan gwamnati na Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a matsayin halaltaccen wakilan kasar Sin a MDD, da kuma korar wakilan yankin Taiwan daga MDD da dukkan kungiyoyin da ke da alaka da shi”, ya kara da cewa, “Har abada kudurin ya warware batun wakilcin kasar Sin baki daya, ciki har da Taiwan, a MDD.”
Wang ya ci gaba da cewa, kudirin ya bayyana cewa, babu wani abu batun “kasar Sin biyu” ko “kasar Sin daya, Taiwan daya.” (Yahaya).