A jiya Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira ga hadin kai da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya da zai kai ga ci gaban juna da samar da makoma mai kyau.
Wang, wanda kuma shi ne mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ta hanyar sadarwa ta bidiyo a zauren taron duniya na shekarar 2023.
Wang ya ce, Duniya a yau tana wanzuwa ta hanyar sauye-sauyen cikin sauri da ba a taba gani ba a cikin karni, ya kara da cewa, akwai hadarin rarrabuwar kawuna da kuma fada da juna, kuma akwai damammaki a cikin hadin kai da hadin gwiwa, kuma “Zabin da muka yi zai yi tasiri akan tarihi”
Wang wanda ya gabatar da shawarwari mai kunshe da abubuwa hudu a cikin jawabin, ya yi kira ga dukkan kasashe da a hade waje guda da hadin gwiwa wajen neman ci gaban juna da samar da makoma mai kyau.
A karshe, Wang ya yi kira da a tsaya tsayin daka kan ra’ayin bangarori daban-daban, da yin aiki tare don inganta tsarin mulkin duniya. (Yahaya)