Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya kira wani taron manema labarai a yau Talata, a gefen zama na farko na taron majalisar wakilan jama’ar kasar karo na 14, inda ya amsa tambayoyin manema labarai na ciki da wajen kasar, dangane da manufofi da dangantakar Sin da kasashen waje.
A cewar Qin Gang, yayin da aka samu saukin annobar COVID-19 a cikin gida, kasar Sin tana dawo da huldar musaya tsakaninta da kasashen waje, kuma harkokinta na diflomasiyya sun samu karin kuzari, kuma tuni suka aike da sako mai karfi.
Ya kara da cewa, zamanantar da kasar Sin mai yawan al’umma sama da biliyan 1.4, abu ne da ba a taba gani ba a tarihin dan adam, wanda kuma ke da gagagrumar fa’ida ga duniya. Yana mai cewa, manufar zamanatarwar ta dace da yanayin da kasar ke ciki a zahiri.
Bugu da kari, ministan ya ce zamanantar da kasar Sin za ta bunkasa zaman lafiya a duniya da tabbatar da adalci da kuma ci gaba.
Game da huldar dake tsakanin Sin da Amurka, Qin Gang ya bayyana cewa, har yanzu Amurka na yiwa kasar Sin bahaguwar fahimta, inda ta mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar gaba dake yin takara da ita, don haka tana aiwatar da manufar da ba ta dace ba kan kasar Sin. Kuma Qin Gang ya kara da cewa, batun Taiwan yana da muhimmanci matuka ga moriyar kasar Sin, tushe ne mafi muhimmanci ga huldar dake tsakanin ksashen biyu wato Sin da Amurka.
Ban da haka yayin da yake karin haske kan huldar dake tsakanin Sin da Rasha, minista Qin ya yi tsokaci cewa, an kafa huldar dake tsakanin sassan biyu ne bisa tushen rashin kulla kawance, da rashin nuna kiyayya da kuma rashin yin adawa ga bangare na uku, shi ya sa huldar dake tsakanin Sin da Rasha ba ta jawo kalubale ga sauran kasashen duniya baki daya ba. (Fa’iza Mustapha, Jamila Zhou)