Ministan ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana cewa dalilin da ya sa ɗalibai da dama suka kasa samun maki mai kyau a jarabawar JAMB na bana shi ne saboda an hana satar amsa sosai fiye da yadda aka saba a baya.
A cewarsa, sakamakon jarabawar bana ya nuna yadda hukumar JAMB ta ƙara ƙaimi wajen inganta tsarin rubuta jarabawa, musamman ta hanyar amfani da kwamfuta wato CBT, da kuma hana duk wani yunƙurin satar amsa da ɗalibai ke yi a baya.
- Karuwar Tafiye-Tafiye Yayin Hutun Ranar Ma’aikata A Kasar Sin Ya Bayyana Kuzarin Masu Kashe Kudi
- ‘Yansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutane A Katsina
Alausa ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata.
Ya ce a maimakon mutane su ɗauki wannan sakamako a matsayin koma-baya ga ilimi, ya kamata a fahimci cewa waɗanda suka samu sakamako mai kyau sun cancanta ne kuma sun yi jarabawa da gaskiya da riƙon amana.
Ya ƙara da cewa JAMB ta ɗauki tsauraran matakai don tabbatar da adalci da gaskiya a jarabawar, wanda hakan ya taimaka wajen rage satar amsa da ake fama da ita a baya.
A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka zauna jarabawar bana, kusan miliyan 1.53 — wato kashi 78 cikin 100 — ba su samu maki 200 ba.
Sai dai ɗalibai 12,414 kacal suka samu maki 300 ko sama da haka.
Ministan ya jaddada cewa wannan mataki na hana satar amsa zai taimaka wajen samar da ƙaimi na ɗalibai masu ƙwazo da amana, tare da ƙarfafa ingancin ilimi a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp