Ministan ma’aikatar lafiya na kasar Tunisiya Ali Mrabet, ya jinjinawa managartan ayyukan da tawagogin jami’an lafiyar kasar Sin ke gudanarwa a Tunisiya.
Ali Mrabet wanda ya yi tsokacin a jiya Litinin, yayin ganawarsa da tawagar likitocin kasar Sin ta 26, lokacin bikin ban kwana da tawagar da ta kammala aiki a kasar, ya ce daukacin mambobin tawagar jami’an lafiyar Sin da ake turawa kasar sun ci gaba da aiki tukuru, yayin da ake fama da annobar COVID-19, sun kuma ba da gagarumar gudummawa ga harkar kiwon lafiya a Tunisiya.
Ministan ya kara da cewa, Sin ta aike da sama da jami’an lafiya 1,100 kasar Tunisiya cikin sama da shekaru 50, kuma irin namijin kokarin da tawagogin suka yi na kunshe da karkasahi, dake tabbatar da matsayin hadin gwiwar Sin da Tunisiya.
A nasa tsokaci kuwa, jagoran tawagar jami’an kiwon lafiya na kasar Sin Xu Chuyang, cewa ya yi har kullum daukacin ‘yan tawagar, na aiki ne bisa imanin su da kasancewar aikin likita ba shi da shinge, kuma a ko da yaushe kare rayukan jama’a shi ne a gaban komai, don haka suke yin duk mai yiwuwa wajen ba da jinya ga kowa. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)