Babu tantama akan cewar, fasahar zamani ta jima da inganta tsari da fasalin gudanar da harkokin kiwon lafiya ta hanyar sauya tsohon salon adana bayanan majiyata a takardu (file). Amma har yanzu a Nijeriya da tsohon tsarin fayal (file) mai cike tarin kalubale ake amfani wajen adana bayanan majinyata, a maimakon yin amfani da sabon sauyin da fasahar zamani ya zo mana da shi.
Saboda kauce wa afkuwar irin matsalolin da ake samu kan rashin amfani da bayanan majinyaci ta zamani, ministan lafiya da kyautata walwala, Farfesa Muhammad Ali Pate ya himmatu don samar da shirin yin amfani da fasahar zamani a wajen adana bayanan majinyata a daukacin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a Nijeriya.
- Matsin Tattalin Arziki: Yadda Ake Kai Ruwa Rana Tsakanin Masu Gidaje Da ‘Yan Haya
- Rundunar Sojin Nijeriya Ta Fitar Da Sunayen Wadanda Ake Zargi Da Kashe Sojoji A Delta
A cewar sashin yanar da ke tallata ayyukan ministan, “A karkashin wannan sabon tsari, babu yadda za a yi a nemi bayanin majinyaci a rasa, domin tsarin ya tanadar da hikimar adana bayanan majinyata a na’ura mai kwakwalwa ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.”
“Babban abin da zai kara kayatar da kai da wannan sabon shirin shi ne, idan asibiti ta dauki bayananin majinyaci tare da adanawa a na’ura mai kwakwalwa, to dukkan wata asibiti da majinyacin ya ziyarta fadin Nijeriya domin ganin likita, da su samu bayanansa a na’ura mai kwakwalwa. Ma’ana, ba sai majinyacin ya sake kashe kudade a wajen gudanar da sabbin gwaje-gwaje da bude fayal ba.”
“Idan shirin ya fara aiki gadan-gadan, za a rika samun sahihan bayanan majinyata a asibitoci a duk lokacin da bukatar haka ya taso. Kana kuma, irin yawan makudan kudaden da gwamnati ke kashewa a wajen buga takardun daukan bayanan majinyata, zai takaita.
“Bugu da kari, shirin zai taimaka ma gwamnati wajen samun sahihan bayanan cuttuka domin daukar matakai a hukumance.”