Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya gudanar da wata gagarumar ziyara tare da jami’an Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a cibiyoyin kiwon lafiya da ke birnin Makkah, a Saudiyya.
Wannan mataki na nuna jajircewar Gwamnatin Tarayya wajen inganta kiwon lafiyar alhazai.
- Mutane Miliyan 9 Na Iya Kamuwa Da Cutar HIV Saboda Rashin Tallafi
- Fursunoni 12 Sun Tsere Daga Gidan Yari A Jihar Kogi
A yayin ziyarar da ya kai ofishin NAHCON a Ummul-Jud, Minista Pate, ya tabbatar da goyon bayan gwamnati domin magance matsalolin kiwon lafiya da alhazai ke fuskanta.
Ya ce wannan shiri na daga cikin ƙudirin Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta jin daɗin mahajjata.
“Sadaukarwarmu tana nan a bayyane,” in ji Minista Pate.
“Duba da yanayin kiwon lafiya a duniya tun bayan ɓullar cututtuka kamar sanƙarau da Shan Inna, wajibi ne mu bi ƙa’idojin kiwon lafiya na Saudiyya.
“Dole ne mu tabbatar da cewa dukkanin alhazai sun samu takardun rigakafi da katin shaidar lafiya,” in ji shi.
Ministan, tare da rakiyar wasu manyan jami’an ma’aikatar lafiya, sun duba motocin ɗaukar marasa lafiya na NAHCON, kayan magani, da shirye-shiryen kiwon lafiya a asibitocin Nijeriya da ke Saudiyya.
Sun gano muhimman wuraren da ake buƙatar ingantawa, ciki har da wadatar magunguna, alluran rigakafi, na’urorin likitanci, da motocin ɗaukar marasa lafiya.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yaba da shirin Ministan, inda ya ce: “Ziyararku ta ƙara mana ƙwarin gwiwa a ƙoƙarin da muke yi na inganta kiwon lafiyar alhazai.”
A duk shekara, kimanin ‘yan Nijeriya 70,000 ne ke halartar aikin Hajji, kuma Ministan Pate ya bayyana damuwarsa kan matsalolin da ke tattare da yanayin zafi mai tsanani da ake tsammanin fuskanta a Hajjin 2025.
Ya ce an ɗauki matakan kariya don tabbatar da lafiyar alhazai da jin daɗinsu.
Wannan shiri na haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Lafiya da NAHCON zai tabbatar da cewa mahajjatan Nijeriya sun samu ingantacciyar kulawa.
NAHCON ta kuma tabbatar da ƙudirinta na ci gaba da samar da ingantattun ayyuka ga alhazai.
Waɗanda suka halarci wannan ziyarar sun haɗa da Minista Pate, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Kwamishinan Ayyuka Prince Anofi’u Olanrewaju Elegusi, Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal, Prince Abdul-Razak Aliyu, Dokta Sa’edu Ahmad Dumbulwa da sauran manyan jami’ai na NAHCON da Ma’aikatar Lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp