Ministan dunkulewar tattalin arziki, kananan kasuwanci, samar da ayyukan yi da fasahohi na kasar Morocco Younes Sekkouri ya bayyana cewa, kasar Sin tana da muhimmiyar rawar da za ta taka a wannan mawuyacin lokaci na farfadowar tattalin arzikin duniya, ba wai kawai a matsayin injiniyan din raya tattalin arziki ba, har ma a matsayin abokiya mai adalci da rikon amana.
Ya kuma bayyana imanin cewa, kasar Sin tana daya daga cikin muhimman injunan raya tattalin arziki a duniya, baya ga zama ginshikin raya tattalin arziki mai adalci, ministan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua haka ne a gefen taron shekara-shekara na dandalin tattauna tattalin arziki na duniya karo na 14 ko taron Davos na yanayin zafi, wanda ake gudanarwa yanzu haka a birnin Tianjian na kasar Sin daga 27 zuwa gobe Alhamis 29 ga watan Yuni.
Batun nuna adalci a dunkulewar duniya, yana daga cikin abin da aka tattauna a dandalin. Da yake tsokaci game da irin abubuwan da ya gani da kuma abin da ya koya, ministan ya ce ya yi imanin cewa, kasar Sin, a matsayinta na daya daga cikin manyan kasashe masu samar da kayayyaki da kwastomomi a duniya, za ta iya zama mai sa kaimi ga tabbatar da daidaito a fadin duniya. (Mai fassarawa: Ibrahim)