Yau ne, ministan tsaron kasar Sin Wei Fenghe, ya gabatar da jawabi kan ra’ayin kasarsa, game da odar yankin a yayin taron tattaunawa na Shangri-La karo na 19 da aka gudanar a kasar Singapore.
Dangane da huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, ministan tsaron kasar Sin din ya ce, yanzu huldar da ke tsakanin kasashen 2 tana cikin wani muhimmin lokaci.
A ganin kasar Sin, kyakkyawar huldar da ke tsakaninta da Amurka ta dace da muradunsu da ma duniya baki daya. A matsayinsu na muhimman kasashe 2 a duniya, ba za a iya raba hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka daga bunkasar duniya cikin lumana ba. Yin fito-na-fito a tsakanin Sin da Amurka ba zai kawo musu da ma kasashen duniya alheri ba.
Kasar Sin tana adawa da ayyana kasashen 2 a matsayin masu takara da juna. Idan Amurka ta ci gaba da mayar da kasar Sin tamkar barazana, abokiyar takara, da ma abokiyar gaba, to, za ta yi mummunan kuskure.
Wei ya nuna cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta dakatar da shafa mata kashin kaji, da neman dakile ci gaban ta, kana ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da kuma illanta muradun kasar Sin.
A bayyane kasar Sin ta bayyana matsayinta, wato wajibi ne Sin da Amurka su tattauna da juna, su mutunta juna, su kuma yi zama tare cikin lumana, su hada kansu domin samun moriyar juna, amma idan Amurka tana son yin fito-na-fito da Sin, to, kasar Sin ba za ta ja da baya ba. (Tasallah Yuan)