Ministan tsaron kasar Sin janar Dong Jun ya bayyana cewa, sojojin kasar Sin a shirye suke a ko yaushe wajen cimma burin kammala sake hadewar kasar Sin baki daya, yana mai yin alkawarin jajircewa ga tarwatsa duk wani yunkurin ‘yan aware na neman ‘yancin kan Taiwan, da dakile duk wani tsoma baki ta fuskar soja daga kasashen waje.
Dong ya bayyana hakan ne jiya Alhamis a wata gagarumar liyafar da ma’aikatar tsaron kasar ta gudanar a birnin Beijing domin murnar cika shekaru 98 da kafuwar rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin wato PLA, wanda ake bikinta a yau 1 ga watan Agusta.
- Zhao Leji Ya Yi Jawabi A Babban Taron Shugabannin Majalisun Kasa Da Kasa Karo Na 6
- Sin Ta Samarwa Sassan Kasa Da Kasa Damar Shigowa Ba Tare Da Bukatar Biza Ba
A ranar 3 ga watan Satumba, kasar Sin za ta gudanar da wani faretin soji a dandalin Tian’anmen na birnin Beijing, domin murnar zagayowar ranar samun nasara a yakin turjiyar al’ummar Sinawa ga hare-haren zaluncin Japanawa da kuma yaki da mulkin danniya a duniya.
Dong ya ce, faretin zai nuna wa jam’iyya da jama’ar kasar Sin cewa, PLA wata runduna ce dake kiyaye zaman lafiya da adalci, kuma ta yi fice ta fuskar karfin soja.
Har ila yau, ya bayyana cewa, sojojin kasar Sin suna son yin aiki tare da takwarorinsu na dukkan kasashen duniya, don cimma burin samar da al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama, da manyan shirye-shiryen samar da ci gaban duniya guda uku, da magance barazanar rashin tabbas da kalubale, da gina duniya mai dauwwamammen zaman lafiya, da samar da tsaron duniya na bai-daya, da wadata tare da bude kofa da damawa da kowa da kowa, da kuma tabbatar da samun kyakkyawan muhalli mai tsabta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp