Ministan harkokin wajen Angola Téte António ya bayyana yayin wata zantawa da ya yi da kafofin watsa labarai a birnin Beijing cewa, tun bayan da aka kulla dangantakar abokantaka tsakanin kasashen Angola da Sin yau shekaru 40 da suka gabata, dangantakarsu ta sami ci gaba sosai, manyan ababen more rayuwa da kamfanonin Sin suka gina a kasar Angola sun riga sun zama daya daga cikin “abubuwan alfahari na kasar”, wanda shi ne tushen inganta ci gaban kasar Angola.
Bisa kididdigar da ofishin jakadancin Sin dake kasar Angola ya bayar, an ce kamfanonin Sin sun gyara ko gina layoyin dogo masu tsawon kilomita 2800, da hanyoyin mota masu nisan kilomita dubu 20, da gina gidaje fiye da dubu 100, da makarantu sama da 100, da asibitoci fiye da 50. Kawo yanzu yawan kamfanoni masu jarin kasar Sin dake kasar Angola ya zarce 400. (Safiyah Ma)