Kwanan baya, wakiliyar CMG ta zanta da ministan harkokin wajen kasar Hungary SZIJJÁRTÓ Péter, inda ya bayyana cewa, bai kamata a dauki kasar Sin a matsayin kalubale ko barazana ba, yana mai cewa, zai fi dacewa a hada kai da ita don samun bunkasuwa tare.
Ya ce: “Yadda kasarmu ta tabbatar da wannan ra’ayi shi ne, nuna adalci da daidaito ga kasar Sin, abin da ya ja hankalin masu zuba jari na kasar. Matakin da kuma ya ingzia bunkasuwar tattalin arzikin kasar da samar da karin guraben aikin yi da ma kyautata rayuwar jama’a, har ma da samarwa kasar fasahohin zamani. Mun sheda cewa, hadin kai da kasar Sin zai kawo dimbin alfanu ga kasarmu a maimakon jayayya da ita”. (Amina Xu)