Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jajanta wa al’ummar Musulmin garin Minna da Gwamnatin Jihar Neja bisa rasuwar Babban Limamin Masallacin Minna, Sheikh Isah Fari.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin sa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabiu Ibrahim ya fitar, ministan ya bayyana marigayi Sheikh Fari wanda ya rasu yana da shekaru 93 a duniya a matsayin babban malamin addini wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen bautar Allah, yaɗa Musulunci, da kuma inganta zaman lafiya a Jihar Neja da ma ƙasar baki ɗaya.
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci ‘Yansanda Su Rungumi Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa
- ‘Yan Bindiga Sun Kone Gonakin Manoma A Zamfara
Ya ce: “Marigayi Sheikh Isah Fari ya nuna maƙasudin addinin Musulunci, wanda shi ne fifikon zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma, ta yadda a shekarun da ya yi yana matsayin Babban Limamin Babban Masallacin Minna an ɗauke shi a matsayin wanda ke jaddada zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Neja.”
Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Umaru Bago, da Sarkin Minna, Alhaji Dakta Umar Faruq Bahago, tare da jaddada gagarumar gudunmawar da marigayi Babban Limamin ya bayar wajen bunƙasa zamantakewa da tattalin arzikin Masarautar Minna da Jihar Neja.
Ya ce: “Ina miƙa alhini na ga Gwamnan Jihar Neja, Mai Girma Umaru Bago, da Sarkin Minna, Mai Martaba Sarkin Minna, Alhaji Dr Umar Faruq Bahago, bisa rashin wani masani wanda ilimin sa ya zame tushe na shawarwari masu inganci don cigaban zamantakewa da tattalin arzikin masarautar Minna da Jihar Neja baki ɗaya.”
Ministan ya buƙaci al’ummar Jihar Neja da su kiyaye koyarwar soyayya, haƙuri da juna da haɗin kai da Sheikh Fari ya bayar a lokacin rayuwar sa, tare da yin addu’ar Allah ya jiƙan marigayin.