Ministocin gwamnatin Tinubu za su fara gabatar da ayyukan da suka yi ko suka sa a gaba a Tarukan Manema Labarai na Ministoci na shekarar 2025 a ranar Juma’a, mai zuwa, 21 ga Fabrairu.
Ma’aikatar Yaɗa da Wayar da Kai ce ta ba bayyana hakan, ta ce za a fara taron da ƙarfe 11 na safe a Cibiyar Manema Labarai ta Ƙasa da ke Abuja.
- An Bude Cibiyar Horar Da Malaman Harshen Sinanci A Ghana
- ‘Yansanda Sun Kwato Motoci 7 Da Aka Sace Da Taimakon Na’urar e-CMR A Kano
Ma’aikatar ta ce bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ministocin za su gabatar da rahoto kan nasarori, manufofi, da shirye-shiryen da suka aiwatar a ma’aikatun su.
Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a.
Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh.
Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba ɗaya don halartar wannan muhimmiyar tattaunawa da nufin bayyana wa jama’a irin cigaban da gwamnati ke samu.