Bayan gama tattaunawar Beijing tsakanin manyan jami’an kasashen Saudiyya da Iran a ranar 10 ga watan Maris, ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Faisal bin Abdelaziz Al Saud, da takwaransa na kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian, sun gana da juna yau Alhamis a birnin Beijing, kuma wannan ne karo na farko da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka gana da juna a hukumance a cikin shekaru 7 da suka gabata.
A karkashin kokarin da kasar Sin ta yi, Sin da Saudiyya da Iran, sun bayar da sanarwar bangarorin uku a watan Maris a Beijing, wadda ke cewa Saudiyya da Iran, sun cimma yarjejeniya a tsakaninsu, wadda ta kunshi yarda da maido da huldar diplomasiyya tsakaninsu, da sake bude ofisoshin jakadanci, da hukumomin wakilai cikin watanni biyu, da kuma tura wa juna jakadu.
An ruwaito cewa, kafin sun isa Beijing, ministocin harkokin wajen Saudiyya da Iran, sun riga sun buga wa juna waya sau da dama, inda suka tattauna yadda za a maido da huldar diplomasiyya tsakanin kasashen 2, da kuma matakan da za a dauka wajen kaddamar da wasu sauran yarjejeniyoyi. (Safiyah Ma)