Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Kamaru Lejeune Mbella Mbella a jiya Jumma’a, wanda ya je Hong Kong don halartar bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa hukumar shiga tsakani ta kasa da kasa mai lakabin “IOMed” a Turance.
A yayin ganawar, Wang ya nuna jin dadinsa kan yadda kasar Kamaru ta taka rawar gani a shirye-shiryen kafa hukumar ta IOMed, kana ya bayyana fatan ganin Kamaru ta amince da abubuwan da taron ya cimma da wurwuri.
A nasa bangaren, Mbella ya ce, shawarar da kasar Sin ta bayar ta kafa hukumar ta IOMed, ta nuna himma da tasirinta, kuma ta yi daidai da ruhin yarjejeniyar kafuwar MDD. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














