Hukumar daidaita al’amuran wutar lantarki ta kasa (NERC), ta ankarar da ‘yan Nijeriya; musamman masu amfani da mitocin wutar lantarki, dangane da fuskantar barazanar daina aiki a watan Nuwamban 2024.
Bayan ayyana barazanar da hukumar ta yi na daina aikin mitocin a shekara mai zuwa, sai ga wasu daga cikin kamfanoni masu kula da rabon wutar lantarkin (DisCos), sun ja hankalin masu amfanin da mitocin cewa, akwai yiwuwar daga nan zuwa karshen wannan shekara mitocin za su daina aiki kwata-kwata, ta yadda ko kudi ba za a iya sanya musu ba.
Kamar yadda LEADERSHIP ta rawaito, Hukumar daidaita al’amuran wutar lantarkin, ta shawarci kamfanonin masu kula da rabon wutar lantarki, da su gaggauta wayar da kan kwastomominsu wajen sake sabunta mitocinsu, domin ci gaba da aiki kamar yadda suka saba, idan kuma ba haka ba; za su fuskanci mummunan kalubale wajen sanya musu kudi daga nan zuwa shekara mai zuwa.
A wata sanarwa da hukumar kula da rabon wutar lantarkin ta fitar a shafinta na Twitter, ta bayyana sake sabunta mitocin a matsayin kyauta ba tare da biyan ko sisin kwabo ba, illa kawai dai masu amfani da mitocin za su ziyarci kamfanonin kula da rabon wutar, domin nuna musu yadda za su sake sabunta su.
“idan kana da mita, magana ce kawai ta yadda za ka sake sabunta ta; ta ci gaba da yin aiki. Daga watan Nuwamban 2024, akwai yiwuwar ba za ka sake iya sanya wa mitarka kudi ba. Sannan, sake sabunta tan abu ne mai matukar sauki kuma kyauta.”
Har ila yau, “Kamfanonin rabon wutar lantarkin, akwai wasu lambobi da za su bayar a matsayin mabudi, wadanda za a yi amfani da su don sake sabunta mitocin kuma kyauta ba tare da kowa ya biya ba,” a cewar hukumar daidaita al’amuran wutar lantarki din.
Bugu da kari, “sabunta mitarka, ba zai shafi kudin da ke cikin ta ba, ko kwabonka ba zai yi ciwon kai ba, sannan ba zai kuma sa mitar ta kara sauri ko gudu ba, dazarar kuma ka ga daya cikin biyun, sai ka garzaya domin yin korafi a a ofishinsu mafi kusa a gyara maka,” a cewar tasu.
Haka zalika, kamar yadda reshen Ikeja na kamfanin kula da rabon wutar lantarkin, karkashin hukumar daidaita al’amuran wutar lantarki ya bayyana, kafatanin mitocin wutar lantarki ta duniya ciki har da Nijeriya, na fuskantar barazanar tsayawa tare da daina aiki a 24 ga watan Nuwamban 2024, sannan duk wanda bai yi kokarin sake sabunta mitar tasa ba, yana cike da barazanar zama cikin duhu daga 1 ga watan Nuwamban 2023.
Kamfanin rabon wutar lantarkin ya ci gaba da bayyana cewa; tuni ya gama shiryawa tsaf domin tunkarar wannan matsala. Hakan kuwa, ta faru ne sakamakon hobbasar da wani kamfani mai kula da sarrafa mitoci a Nijeriya ya yi (MOJEC), domin tallafa wa kamfanonin rabon wutar lantarki a Nijeriya, domin sake sabunta mitoci don amfanin ‘yan kasa baki-daya, musamman masu amfani da ita.
Manajan Daraktan Kamfanin Mita na MOJEC, Madam Chantelle Abdul, ta sake tabbatar da tabbacin bayar da wa’adin na barazanar daina aikin mitoci a Nijeriya, daga watan Nuwamban 2024 ba 2023 da wasu ke shelantawa ba.
Ta kara da cewa, hukumar daidaita al’amuran wutar lantarki (NERC), ita ce ke da alhakin kula tare da baiwa kamfanonin rabon wutar lantarkin da kuma na masu sarrafa mitoci umarni, musamman a wannan gaba da ake fuskantar barazana na daina aikin wadannan mitoci.
A cewar tata, umarnin a halin yanzu ya hada da tabbatar da ganin sabbin mitocin da za a samar na dauke da tsarin sabunta mitar na 2024, ba kuma daga bisani a ce sai an sake sabunta su ba.
Sannan, ta kara jan hankalin kananan kamfanoni masu tasarrafi da mitoci, da su tabbatar sun sabunta su kafin su sayar wa masu amfani da su kafin 2024. “Da zarar kamfanonin rabon wutar lantarki (Discos), sun sabunta wadannan mitoci, wajibi ne su ma sauran kananan kamfanoni masu tasarrafi da mitocin su sabunta su kafin kai wa ga sayarwa da mutane.
Kamar yadda rahoto ya bayyana, kamfanonin rabon wutar lantarki, sun samar da akalla mitoci 171,107 ga kwastomominsu a watanni hudun farkon wannan shekara ta 2023.
Haka zalika, rahoton ya kara nuni da cewa, a cikin mutane miliyan 12.38 da suka yi rijista don neman mita, miliyan 5.36 ne kacal suka samu. “A 31 ga watan Mayun 2023, wadanda suka nemi mita sun kai miliyan 12,378,243, amma miliyan 5,360,434 ne kadai sukaa samu.
A farkon wannan shekara, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin samar da mitoci kimanin miliyan shida a duk fadin Nijeriya, a watanni hudun farko da na tsakiyar shekarar, domin sake rage yawan wadanda ba sa amfani da mitar a fadin kasar.
An bayyana hakan ne a watan Disambar 2022, a yayin sake tantance ayyuka tare da dora ayyukan da ma’aikatar kula da wutar lantarki ta kasa ta yi karkashin kulawar wannan gwamnati a sikeli.
Har ila yau, ma’aikatar kula da wutar lantarkin ta kasa, ta bayyana nasarar da ta samu na samar da akalla mitoci miliyan daya, a shirnta na kokarin wadata kasa da mitoci.
Haka zalika, Babban Bankin Nijeriya na Kasa tare da Hukumar daidaita al’amuran wutar lantarki, su ne kinshikai wajen tabbatar da nasara, tsarawa da kuma tabbatar da shirin.