Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa kungiyar Miyetti Allah, za ta taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Abubakar ya ce shugabancin MACBAN na iya taimakawa wajen kawo karshen matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a Najeriya.
- Mata Da Yara Akalla 721 Aka Yi Wa Fyade Cikin Watanni 9 A Kano
- NDLEA Ta Yi Nasarar Cafke Wani Shugaban Masu Safarar Kwaya Da Take Nema Ruwa A Jallo
Ya yi wannan tsokaci ne a lokacin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar na kasa ta MACBAN a babban masallacin kasa Abuja.
A baya-bayan nan dai ana alakanta Fulani makiyaya da yin garkuwa da mutane da yin fashi a kasar.
Ana zargin Fulani makiyaya da kai hare-hare kan manoma da sauran daidaikun jama’a.
Hare-haren ‘yan bindiga ya yi sanadiyyar salwantar rayukan dubban mutane da kuma tilasta wasu yin kaura daga muhallansu.