A yau Litinin, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta tabbatar da cewa, mizanin GDPn kasar Sin ya karu da kaso 5.5 bisa dari a farkon rabin shekara ta 2023.
Alkaluman hukumar ta NBS sun nuna cewa, a zangon farko na wa’adin, darajar GDPn na Sin ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 59.3, kwatankwacin dalar Amurka kusan tiriliyan 8.3. Kaza lika a rubu’i na biyu, GDPn ya bunkasa da kaso 6.3 bisa dari.
Da yake tabbatar da hakan yayin taron manema labarai da ya gudana, kakakin NBS Fu Linghui, ya ce rabin farko na shekarar nan, lokaci ne da sassan kasa da kasa suka sha fama da ayyuka masu sarkakiya na aiwatar da sauye-sauye, da samar da ci gaba da daidaito a cikin gida, kana dukkanin yankuna da sassan hukumomi sun yi matukar kokarin wanzar da daidaito, da samar da guraben ayyukan yi, da daidaita farashin hajoji.
Har ila yau, Fu Linghui ya ce sannu a hankali bukatun kasuwa na kara farfadowa, kuma ana samun karuwar samarwa da rarraba hajoji, da kara kyautatuwar sassan tattalin arziki.(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp