Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin, sun nuna cewa ya zuwa watan Oktoban da ya shude, alkaluman gudummawar masana’antun kasar Sin ga mizanin GDPn kasar, wanda ke matsayin muhimmin mizanin awon bunkasar tattalin arzikin kasar, ya karu da kaso 5.3 bisa dari a shekara.
Alkaluman hukumar na wata-wata da ta fitar a yau Juma’a, sun nuna yadda a watan Oktoba kadai, mizanin hajoji da hidimomi da masana’antun kasar Sin ke samarwa ya karu da kaso 0.41 bisa dari kan na watan Satumba. Yayin da alkaluman suka karu da kaso 5.8 bisa dari tsakanin watan Janairu da Oktoban bana, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
A daya hannun, alkaluman hukumar sun nuna yadda jarin kadarori dake jimawa a ajiye suka karu da kaso 3.4 bisa dari a shekara, cikin watanni 10 na farkon shekarar nan ta 2024. Har ila yau, alkaluman nazarin mizanin yawan rashin guraben aikin yi a biranen kasar Sin ya tsaya kan kaso 5.1 bisa dari tsakanin watannin 10, wanda ya ragu da kaso 0.2 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara. (Saminu Alhassan)