Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Luka Modric ya bayyana cewa, zai bar kungiyar kwallon kafa ta kasar Sifaniya bayan kammala gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa ta Fifa a bana.
Dan wasan tsakiyar Croatia, mai shekara 39, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2018, zai buga wasansa na karshe a gidan Real Madrid (Bernabeu) a ranar Asabar, inda za su kara da Real Sociedad a wasan karshe na gasar La Liga.
- Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin
- Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai
“Lokaci ya zo, lokacin da ban taba son zuwansa ba, amma wannan shi ne kwallon kafa, kuma a rayuwa komai yana da mafari da karshe,” in ji Modric a Instagram.
Modric, ya lashe kofuna 28 da suka hada da gasar zakarun Turai 6 da Laliga 4 tun lokacin da ya koma Real daga Tottenham a shekarar 2012.
“Na zo ne a shekarar 2012 tare da fatan sanya rigar yan wasan da suka fi fice a duniya da kuma burin samun manyan nasarori, Real Madrid ta canza rayuwata a matsayina na dan wasan kwallon kafa da kuma mutum, ina alfahari da kasancewata a daya daga cikin mafi kyawun kulob a tarihi” inji shi.
Real za ta bude gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa da Al-Hilal ta Saudi Arabiya a ranar 18 ga watan Yuni, sannan kuma za ta kara da Pachuca ta Mexico da RB Salzburg ta Austria a matakin rukuni.
Modric ya ci kwallaye biyu sannan ya taimaka aka ci shida a wasanni 34 da ya buga a gasar ta Sifaniya a kakar wasa ta bana, yayin da Barcelona ta lashe gasar.
Wasan na ranar Asabar, shi ne na karshe da Ancelotti zai jagoranci Real, inda aka ruwaito kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso zai maye gurbin kocin dan kasar Italiya, shugaban kulob din Florentino Perez. A cikin wata sanarwa da ya fitar yana cewa, “Modric zai kasance har abada a cikin zukatan dukkan Madridistas a matsayin dan wasan kwallon kafa na musamman kuma abin koyi wanda a ko da yaushe ya kasance yana kunshe da kimar Real Madrid.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp