Alkaluman da kungiyar masana’antun kera motoci ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin sun nuna cewa, motocin da Sin ta samar sun kai miliyan 31.282, wadanda kuma ta sayar su ma sun kai miliyan 31.436, inda aka samu kari da kashi 3.7 cikin dari da kuma kashi 4.5 cikin dari bisa makamancin lokacin na shekarar 2023, wanda ya kafa sabon tarihi.
Daga cikinsu, yawan motocin dake amfani da sabbin makamashi ya zarce miliyan 12, wanda ya zama na farko a duniya tsawon shekaru goma a jere.
Bugu da kari, kasar Sin ta rika fitar da motoci miliyan 5.859 zuwa kasashen waje a duk shekara, adadin da ya karu da kashi 19.3 cikin dari bisa makamancin lokacin na shekarar 2023, wanda shi ma ya zama na farko a duniya.(Safiyah Ma)