Adadin motocin sabbin makamashi da ake amfani da su a kasar Sin na ci gaba da karuwa cikin hanzari, inda yawansu ya kai miliyan 31.4 zuwa karshen 2024, kamar yadda ma’aikatar kula da tsaron jama’a ta sanar a yau Juma’a.
Adadin ya nuna karuwarsu da ninkin-ba-ninki sau 260 cikin shekaru goma da suka gabata, wanda ake ta’allakawa da ci gaban da aka samu a bangaren fasahar masana’antar kera motocin sabbin makamashin, da inganta kayayyakin cajinsu da kuma karuwar wayewar kan Sinawa a kan kiyaye muhalli, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.
Ma’aikatar tsaron ta kuma kara da cewa, a shekarar 2024, motocin sabbin makamashin sun kai kashi 8.9 na daukacin adadin motocin da ake da su a kasar, yayin da adadin sabbin da aka yi musu sabuwar rajista na motocin sabbin makamashin ya karu da kashi 51.49, idan aka kwatanta da na shekarar 2023, wato adadin ya kai miliyan 11.25. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)