Shugaban Masallatan harami, Sheikh Abdulrahman Sudais, ya shawarci musulmai da ci gaba da dabbaka kyawawan ɗabi’u a duk rayuwarsu kamar yadda suka yi a watan Ramadan.
Sudais ya yi wannan kiran ne a yayin nasihar da ya fitar ta bankwana da Azumin Ramadan na shekarar 1446/2025.
- Tawagar Ma’aikatan Ceto Ta Kasar Sin Ta Isa Birnin Yangon Na Kasar Myanmar
- Shugaba Xi Ya Jajantawa Shugaban Myanmar Game Da Girgizar Kasar Da Ta Auku
Daga cikin Nasihar, Shugaban ya yi kira da Azumtar kwanaki shida acikin watan Shawwal, wanda sakamakon hakan ke nunin cewa, kamar Azumin tsawon shekara ne.
Annabi (saw) ya ce: “Wanda ya azumci Ramadan, kuma ya bi shi da kwanaki shida na Shawwal, kamar ya azumci shekara ne.” Muslim ne ya ruwaito Hadisin
Ku kasance masu tausasawa da rahama, ku sadar da zumunta, ku sanya farin ciki azukatan al’umma kuma ku yada farin ciki, sannan ku nemi kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ji da ɗa’a ga umarnin shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp