Zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jama’are/Itas Gadau, Bala Rabili Kashuri na jam’iyyar APC, ya ce nasara tasa ce ko da masu adawa sun garzaya kotu don kalubalantar nasararsa.
A cewarsa, al’ummar mazabar sun amince masa duba da kyawawan manufofin da ya zo da su kuma da yardar Allah kotu za ta tabbatar masa da nasararsa.
- ‘Yan Siyasa Ne ke Kokarin Raba Kan ‘Yan Nijeriya —Solomon Dalong
- An Kama Mutane 3 Kan Zarginsu Da Hannu A Kisan Wasu 2 A Kaduna
Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Da yake zantawa da manema labarai a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a hanyarsa ta tafiya Umarah, ya ce abokin takararsa ya kai kara kotu, inda yake korafi kan nasaran da ya samu.
“Wannan hidima ce ta siyasa ba za ka kayar da mutum ba kuma ka hana shi kuka ba.
“Saboda haka ina amfani da wannan dama na yi kira ga dukkan jama’armu ta mazabar Jama’are/Itas Gadau su kwantar da hankalinsu yadda Allah ya ba mu nasara a zaben fidda gwani muka yi nasara kuma muka yi nasara a zabe, haka in sha Allah mu ne da nasara a kotu.”
Kashuri ya yi kira zuwa ga al’ummar mazabarsa da su yi amfani da wannan dama a watan Ramadan domin yin addu’o’i ga kasa.
Daga bisani zabebben dan majalisar ya gode wa jama’ar mazabarsa bisa zabarsa da suka yi da ba shi goyon baya.