Tsohon ministan harkokin matasa a Nijeriya Barrister Solomon Dalong ya bayyana muhimmancin dake akwai ga al’ummar Nalijeriya mabiya Addinin Kirista da Musulunci su zauna lafiya da juna.
Tsohon ministan ya yi wannan bayanin ne a wurin wani taron cin abincin da shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi ya saba shiryawa kowace shekara a Jihar Kaduna.
Ya kuma jaddada cewa, kasancewar Allah ya kasa al’ummar Nijeriya masu Addinai daban-daban kuma karkashi kabilu mabanbanta alheri ne da ya kamata mu ribace shi ta hanyar hada kawunanmu.
Ya yi bayani a game da babban zaben kasar da aka gudanar tsakanin watan biyu da watan jiya inda ya ce duk da cewa an kammala zabe, zaben ya bar baya da kura kuma kamata ya yi mutane su kiyaye duk wani abin da zai raba kansu.
Shararren Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Bauchi a cikin jawabinsa a wurin taron, ya ce duk dan siyasar da zai hada kan al’umma ba tare da nuna banbanci ba, shi ya dace da shugabancin Nijeriya, kana ya nuna cewar Allah ya hallice mu domin mu fahimci juna sannan mu taimakawa juna ba domin raba kawunan mu ba kuma ya ce duk wanda yake ji ba a yi masa adalci ba a zaben da aka gudanar, kotu ce sahihin hanyar da doka ta tanadar domin neman hakkin mutum.
Fasto Yohana Buru wanda shi ma ya hallarci taron cin abincin da aka yi a gidan shahararren mallamin, ya ce kamata yayi mutane su yi wa Allah godiya da ya yadda Allah ya hallice mu kuma su fahimci masu neman janyo rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.