A cikin shekarar 2022, shugabannin Sin da Rasha sun gana a birnin Beijing na kasar Sin a yayin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, shugabannin Sin da Amurka sun gana a tsibirin Bali, kana akwai ganawa tsakanin shugaban Sin da shugabannin kasashen Faransa, da Jamus da sauransu, wadanda suka shaida cewa, Sin ta sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa.
A karkashin jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, a cikin shekarar da ta gabata, Sin da Rasha sun nuna goyon baya ga juna wajen kiyaye muhimman moriyarsu, da kara yin imani da juna kan harkokin siyasa da manyan tsare-tsare, da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. Dangantaka tsakanin Sin da Rasha bisa tushen nuna daidaito da nuna adawa da kafa wani gungun kawance da rashin nuna kiyayya da juna da kin amincewa ga wani bangare na daban ta kara samun ingantuwa.
Game da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, a yayin ganawar shugabannin Sin da Amurka a tsibirin Bali, shugaba Xi Jinping ya yi bayani a fili game da hakikanin dangantakar Sin da Amurka, da bayyana abin da Sin take adawa, inda ya jaddada cewa, ya kamata a yi watsi da akidar samun nasara daga faduwar wani bangare. Haka kuma ya kamata a rika yin shawarwari da samun moriyar juna, bisa ka’idojin girmama juna da zama tare cikin lumana da hadin gwiwa don samun moriyar juna, an sa kaimi ga maido da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata.
A shekarar 2022, shugaba Xi Jinping ya buga waya ko ganawa fiye da 20 tare da shugabannin kasashen Turai. An kuma samu karuwar zuba jari da cinikayya a tsakanin Sin da Turai, da fara aiwatar da manyan ayyukan dake shafar bangarorin biyu, wannan ya shaida cewa, Sin da Turai abokan hulda ne ba abokan gaba ba, sun kuma samu damammaki maimakon kawo barazana ga juna .
Idan har ana fatan duniya ta gyaru, wajibi ne manyan kasashe su kasance abin misali da daukar nauyin dake bisa wuyansu yadda ya kamata. Domin yadda irin wadannan manyan kasashe ke mu’amula da juna, yana da tasiri sosai kan makomar daukacin bil-Adama. (Zainab)