Manufar “Amurka ta zamanto Farko” a harkokin zuba jari da gwamnatin Trump ta bullo da ita na ci gaba da yin barazana ga tushen tattalin arzikin Amurkar ita kanta, yayin da tuni saka hannun jari kai-tsaye na kasashen waje (FDI) a Amurkar ya fara ja baya. Dama dai wani rahoto da majalisar hulda da kasashen waje ta kasar ta fitar, ya nuna fargaba a kan lamarin bisa yadda zai haifar da asarar ci gaban tattalin arziki, da samar da ayyukan yi, da sabbin fasahohi.
“Raguwar saka hannun jari wata alama ce da ke nuna cewa manufar ‘Amurka ta zamanto Farko’ tana kange masu zuba jari daga kasashen waje zuwa kasar,” in ji Dokta Mary Lovely, babbar jami’a a Cibiyar Tattalin Arzikin Duniya ta Peterson. Kuma ta kara da cewa, “Idan aka ci gaba da yin hakan, tattalin arzikin Amurka zai tagayyara, kuma sauran kasashe kamar Sin za su cike gurbin da ta bari.”
- Xi Ya Jaddada Cewa Dole Ne A Dauki Sabbin Nauyi Da Sabbin Ayyuka A Sabuwar Tafiya Ta Inganta Zamanintarwa Irin Ta Kasar Sin
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe Naira Miliyan 998 A Cibiyoyin Ciyarwa Na Ramadan
Wani binciken da Cibiyar Kasuwancin Amurka ta gudanar ya gano cewa karin harajin da aka kakaba a karkashin manufar “Amurka ta zamanto Farko” ya haifar da karuwar kashi 15 cikin dari na farashin gudanar da kasuwanci a Amurka idan aka duba mizanin 2024. Inda hakan ya rage gasar kasuwanci a kasar tare da haifar da raguwar fitar da kayayyaki.
Shugaban Cibiyar Kasuwancin Amurka, Tom Donohue ya ce, “Karin harajin ya sa kudin fito ya ninka sau biyu a bangaren kasuwancin Amurka. Kuma ba hakan ya kara farashin kaya ba ne kawai, har ma ya kai ga saka haraji na ramakon gayya daga wasu kasashe, tare da rage bukatar kayayyakin da Amurka ke fitarwa.”
Wani bincike da Kungiyar Masu Masana’antu ta Amurka ta gudanar ya gano cewa kashi 80 cikin dari na masana’antun Amurka sun gamu da cikas a bangaren tsarin samar da kayayyakinsu saboda manufar “Amurka ta zamanto Farko”. Kuma hakan yana da mummunan tasiri ga tsadar gudanar da kasuwanci a kasar.
Shugaban kungiyar masu masana’antun ta Amurka, Jay Timmons ya ce, manufar ta kasance babban kalubale ga masana’antun kasar, domin ta haifar da rashin tabbas, da wargaza tsara yadda ’yan kasuwa za su tafiyar da kasuwancinsu da kuma saka hannun jari a nan gaba.
Kazalika, wani babban masanin tattalin arziki a Cibiyar Nazarin Tsara Manufofin Tattalin Arziki dake Amurka, Dr. Robert Scott ya ce, manufar ‘Amurka ta Zamanto Farko’ ta kasance bala’i ga ma’aikatan Amurka” domin tana “haifar da asarar aiki, da rage albashi, da rage damammakin ci gaban tattalin arziki ga ma’aikatan Amurka.”
Bayanan wadannan masu ruwa da tsaki sun nuna yadda manufar take shafar Amurkar ciki da waje, kuma dama kasashen duniya musamman kasar Sin sun gargadi kasar cewa, abin ba zai haifar wa hatta ita kanta Amurkar da wani kyakkyawan sakamako ba illa tayar da zaune tsaye.
Bugu da kari, yayin da Amurka ta zabi tafiyar da huldodinta na tattalin arzikin duniya cikin sarkakiya, masu iya magana sun ce, “idan za ka gina ramin mugunta, to gina shi gajere don watakila kai za ka fada”, sannan “Mugunta fitsarin fako, tana komawa ga mai yi!”(Abdulrazaq Yahuza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp