An shiga mako na 12 ke nan ana tafka zanga-zanga a kasar Isra’ila. Dubban daruruwa mutane ne ke sake fitowa a kowacce rana suna shiga sahun masu zanga-zangar tare da yin Allah-wadai da gwamnantin Benjamin Netanyahu bisa bullo da dokar kwace ikon bangaren shari’a.
Zanga-zangar wacce tunda farko ta soma da mutane kalilan ta fara ci kamar wutar daji a kasar ganin yadda ta soma karbuwa a wurin wasu jami’an gwamnati da ma’aikata da suke adawa da sabuwar dokar da Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya bullo da shi.
Rahotanni daga kafafen watsa labaran kasar sun tabbatarda cewa ya zuwa yanzu muhimman abubuwa sun faru daga farkon zanga-zangar zuwa hada wannan rahoton.
Abubuwan da suka faru sune kamar haka;
- An rufe kafatanin gidajen abinci, cibiyoyin lafiya, ofisoshin gwamnati, ma’aikatar kudi, Babban Bankin kasar Isra’ila, tasoshin zirga-zirga da na ababen hawa, an kulle jami’o’in kasar, wuraren tarihi, shagunan sayayya, da sauran muhimman wurare.
- Â Dukkanin ma’aikatan wadannan wurare sun tafi yajin aiki tare da shiga cikin zanga-zangar da take ci gaba da kazancewa a Haramtacciyar kasar ta Isra’ila.
- Â An rufe ofishin Jakadancin Isra’ila da ke birnin Washington da wasu wuraren hulda da Isra’ila da ke Amurka domin nuna goyon baya ga masu zanga-zangar.
- Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana yi wa masu zanga-zangar barazanar shekar da jinanensu ta hanyar shirin jami’an ko ta kwana. Inda jami’an ke antaya wa masu zanga-zangar ruwan zafi da barkonon tsohuwa tare da dukan masu zanga-zangar.
- Â Masu zanga-zangar na kara yawa a kowacce rana inda bayanai ke tabbatar da cewa dubban daruruwa ne a yanzu ke kira da gwamnatin Netanyahu da ta janye kudurin dokarta, idan ba haka ba za su ci gaba da zanga-zangar har sai mama ta gani.
- Â Masu zanga-zangar na zuwa muhimman wurare a Isra’ila suna shigar da kokensu. A inda suka je har kotun kolin kasar. Zanga-zangar har wala yau ta karade har cikin babbar kasar na TelAbib.
- Kungiyar kwadago mafi girma a kasar ta tafi yajin aiki na kafatanin ma’aikata inda ta bukace su da su tafi yajin aiki da kuma shiga cikin masu zanga-zangar.
- Fiye da shugabannin garuruwa 24 ne suka tafi yajin aikin cin abinci domin tursasawa gwamnatin Netanyahu.
- Asaf Zamir, wanda shi ne Babban Jami’in lura da ofishin Jakadancin Isra’ila na birnin New York ya ajiye aikinsa a wani mataki na goyon bayan masu zanga-zanga tare da Allah-wadai da gwamnatin Netanyahu bisa korar ministan tsaron kasar.
- Ministan kudin Isra’ila cikin firgici ya ce dole ne Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya saurari koken masu zanga-zangar. Inda ya goyi bayan masu zanga-zangar tare da yin kira da masu zanga-zangar su yi tururuwa a birnin Jerusalem. Wannan furuci na sa ya sanya Firaministan kasar Isra’ila, ya sauke ministan tsaron.
- Â Shugaba Biden na kasar Amurka ya ce dole ne hukumomi a Isra’ila su yi takatsantsan tare da yin sulhu da masu zanga-zangar.
- Sai dai sakamakon yadda zanga-zangar kullum take kara tumbatsa a kasar, tare da barbazuwa a sassan kasar daban-daban da kuma matsin lamba da Firaminista Netanyahu ke fuskanta daga ‘yan adawa da jami’an kasar, ya tilasta masa jinkirta kudurin dokar sake yi wa bangaren shari’ar garambawul.
Sai dai masu zanga-zangar sun ce ba jinkirtawa suka bukata daga gare shi ba illa iyaka ya dakatar da kudurin dokar baki daya.